Gwamnan APC ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, rai da rai ga masu fyade

0
30

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya sa hannu bayan amincewa da sabbin dokoki biyar a jihar.

Kamar yadda takardar da Antoni Janar kuma Kwamishinan shari’a ta jihar, Hajiya Rahmatu Adamu Gulma ta gabatar ga manema labarai, tace Mannequin Penal Code 2021 ta tanadar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a jihar Kebbi a karkashin sashi na 247.

Sannan duk wanda aka kama da laifin yin fyade, karkashin sashin doka ta 259 yanki na 1, hukuncin daurin rai da rai ne.

Takardar ta kara da cewa Bagudu a watan Disamban 2020 ya amince da amsar kudaden haraji a jihar da kananun hukumomi dake fadin jihar Kebbi, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan APC ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, rai da rai ga masu fyade

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, wani Keneth Okoro, mai shekaru 45 ya bayyana gaban kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas, bisa laifin garkuwa da yaransa guda 2 wadanda suke hannun mahaifiyarsu.

An ceto wasu daga matasan takum 25 da aka sace

Okoro bai amsa laifinsa ba da ake zargin ya aikata a ranar 19 ga watan Disamban 2020 a layin Atanda dake wuraren Mafoluku a jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Lauyan masu kara, Kehinde Ajayi, ya sanar da kotu cewa mutumin ya sace yarinyarsa mai shekaru 10 da dansa mai shekaru 8 da suke hannun mamarsu.

What's On Your Mind?