Hotuna: Gwamna Zulum ya ba da umarnin sabunta masana’antu 5

0
62

‘Gwamna Babagana Umara Zulum a jiya Litinin ya ba da umarnin sabunta masana’antu 5 wanda a yanzu haka suke aiki amma basa samar kaya yadda ya kamata.

Masana’antun sune masana’antar ‘kyara takalma ta NEITAL wacce ke sarrafa fatun dabbobi, da kuma takalma, sauran masana’antun 4 kuwa suna rukunin masana’antu dake kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu wanda tsohon Gwamna Kashim Shettima, ya samar a lokacin mulkin shi. masana’antu 16 dake rukunin, mafi yawan su suna samar da kayan aikin ruwa, da sauran kayayyakin robobi, da sarrafa kayan amfanin gona iri-iri.

Gwamna Zulum, yayi rangadin masana’antun a birnin Maiduguri a jiya Litinin, ya ce yana da niyyar farfado da masana’antu guda 9 da basu fara aiki ba ko kuma karacin gudanar da aiki.

Gwamna Zulum ya ba da umarnin sabunta masana’antu 5

Akwai masana’antu guda 21 a cikin babban birnin jaha, wasu daga cikin su ko dai basa aiki, ko basu fara ba, ko kuma suna aikin amma basu da karfin samar da kaya yadda ya kamata.

A kokarin da yake na yin amfani da damar da jahar Borno take da shi na hanyoyin samar arziki inda ta hada iyakoi da kasashe uku, Gwaman Zulum ya saka ‘kaimi don farfado da masana’antun da aka barsu basa aiki.

A cikin watan Mayun wannan shekara, bayan rangadin masana’antun dake fadin jahar Borno Gwamnan ya kafa wani kwamiti wanda ya dorawa alhakin nemo hanyoyin da za’a farfado da dukkanin masana’antun dake fadin jaha domin ganin solar fara yin aiki babu kama hannun yaro.

Gwamna Zulum ya ba da umarnin sabunta masana’antu 5

Kwamitin karkashin jagorancin Engr Abatcha Jarawa, wanda shi ne shugaban masana’antar sarrafa robobi ta jahar Borno.

Kalli Bidiyon: Kalli Yadda Tsoron Budurwa Ke Tona Asirin Wasu Shugabannin Arewa

Rangadin gani da ido domin ganin abin da kwamitin suka cimma, Gwamna Zulum ya je masana’antar sarrafa Takalma da jema fata inda ya tarar da masana’antar tana aikin da be taka kara ya karya ba.

Gwamna Zulum ya ba da umarnin sabunta masana’antu 5

Gwamna Zulum ya bada umarnin farfado da sashen sarrafa takalma wanda ba ya aiki, da kuma Sashin da ke sarrafa fatar dabbobi wacce aka shirya don samarwa masana’antu domin ta cigaba da aiki kamar yadda ya kamata. Gwaman Zulum ya ce idan masana’antar tana aiki yadda ya kamata hakan zai samar da damarmakin ayyuka ga matasan jahar Borno.

(*5*)

Gwamna Zulum ya kuma ziyarci rukunin masana’antun 16 na jahar Borno kamar yadda aka fada a baya.

Gwamna Zulum ya ba da umarnin sabunta masana’antu 5

Gwamnan ya ba da umarnin dawo masana’antu 4 kan ganiyar su wanda a yanzu basa aiki kamar yadda ya kamata.

A masana’antar sarrafa robobi Gwamna Zulum ya duba wani bangare na kujerun zaman ‘dalibai sama da 3,000 wanda kamfanin roban jahar Borno ya samar, inda Gwamnan ya nuna gamsuwa da ingancin aikin da ake gudanarwa.

Gwamna Zulum ya kuma yi rangadi zuwa masana’antar sake sarrafa shara ta jahar Borno wacce ke aiki yadda ya kamata.

What's On Your Mind?