Gwamna Yahaya Bello Ya Cancanci Zama Shugaban Nijeriya – Hon Aminu Mustapha

- Advertisement -

Gwamna Yahaya Bello Ya Cancanci Zama Shugaban Nijeriya – Hon Aminu Mustapha

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

An bayyana gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, a matsayin wanda ya cancanci jan ragamar shugabancin Nijeriya a 2023, duba da irin dimbin nasarorin da yake samu a matsayinsa na gwamna.

Mai baiwa gwamnan shawara ta musamman akan baki ko wadanda ba yan kasa ba( S. A on Non Indigenes), Alhaji( Hon) Aminu Mustapha ne ya bayyana hakan, a yayin da yake zantawa da Jaridar MOBILIZED9JA A Yau, a garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Hon Mustapha yace shugabancin Nijeriya na bukatar mutum irin gwamna Yahaya Bello duba da kudurinsa na inganta rayuwar al’ummar jihar Kogi.

Hon Aminu Mustapha wanda ya bayyana dimbin nasarorin da gwamnan ya cimma tun lokacin daya dare kujeran shugabancin jihar ta Kogi, ya kuma kara da cewa gwamna Bello mutum ne wanda idan har aka mika masa ragamar shugabancin kasar nan,to shakka babu, Nijeriya zata kasance daya daga cikin manyan kasashen duniya da suka samu ci gaba ta fannoni da dama na rayuwa.
Mai baiwa gwamnan shawara ta musamman kazalika yace babban kalubalen da kasar nan ke fuskanta a wannan lokaci, shine barazanar sha’anin tsaro, inda yace idan har aka damkawa gwamna Bello akalan shugabancin Nijeriya, lamarin zai zama tarihi ganin cewa mutum ne wanda jiharsa ke kan gaba wajen samar da tsaro a duk fadin kasar nan.

Hon Aminu Mustapha daga nan, a madadin sauran wadanda ba ‘yan asalin jihar ta Kogi ba, ya jaddada biyayyarsu da kuma goyon bayansu ga kuduri da kuma aniyar gwamna Yahaya Bello na tsaya wa takarar kujeran shugabancin Nijeriya.

Hon Aminu Mustapha har ila yau, ya godewa mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji ( Dakta) Muhammadu Kabir Maikarfi 111, a bisa goyon bayan da yake baiwa baki dake jihar, sannan ya kara da cewa Sarkin na Lokoja, yayi matukar farin ciki da nadinsa a matsayin mai baiwa gwamna shawara ta musamman akan sha’anin baki ko wadanda ba yan kasa ba.

- Advertisement -