Gwamna Uzodinma ya na kashewa APC kasuwa a Imo inji Hadimin Okorocha

0
18

Hadimin tsohon gwamnan jihar Imo, Sam Onwuemeodo, ya bayyana abin da ya hana mai gidansa Rochas Okorocha, zuwa wani taro na APC da aka yi.

Kwanan nan wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na yankin Kudu maso gabashin Najeriya solar hadu solar yi wani taro a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Owerri.

Sam Onwuemeodo ya yi bayanin abin da ya sa Rochas Okorocha bai samu halartar wannan taro ba.

Da yake hira da ‘yan jarida a ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020, Sam Onwuemeodo ya zargi gwamna Hope Uzodinma da kashewa APC kasuwa.

Gwamna Uzodinma ya na kashewa APC kasuwa a Imo inji Hadimin Okorocha

Onwuemeodo ya kira wannan taro da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin kasa su ka gudanar a karkashin jagorancin Hope Uzodinma a matsayin shiririta.

Da aka tambayi hadimin Sanatan, sai ya ce: “Mutane nawa ku ka gani a wajen wannan taron? ‘Yan majalisar wakilan tarayyar Najeriy nawa su ka je?

Ya ce: “Kun ga Sanata Rochas Okorocha, Sanata Ifeanyi Ararume, ko Sanata Orji Uzor Kalu da duk manyan shugabannin jam’iyya a wajen wannan taron?

“Kusan shekara guda kenan tun da Hope Uzodinma ya zama gwamna, kuma bai taba kiran wani taron APC a Imo ba. Taron, shirmen ‘yan siyasa ne kawai”

Fittatun Farfesoshin Nigeria 13 da suka rasu a 2020

A cewar Onwuemeodo, nan gaba kadan za a banbamce tsakanin zare da abawa a siyasar jihar Imo

“Duk wadanda su ka kai APC kudu maso gabas ba su wurin taron. Mu na kalubalantar su kawo sakamakon zaben akwatinsu na 2015 da 2019.” Inji Onwuemeodo.

A jiya mun tattaro maku wasu manyan al’amuran siyasa da suka yamutsa hazo a shekarar 2020

Daga ciki har da sauke Adams Oshiomhole daga shugabancin APC da rikicinsa da Godwin Obaseki da kuma sake naɗa shugaban hukumar zabe da aka yi

Haka zalika mun kawo maganar rikicin Bala Muhammad da Yakubu Dogara a Bauchi da kuma sauyin-shekar wasu ‘yan siyasa irinsu Sanata Elisha Abbo.

What's On Your Mind?