Gwamna Neja Ya Taya Gwamna Lalong Murnar Cika Shekara 58

- Advertisement -

Gwamna Neja Ya Taya Gwamna Lalong Murnar Cika Shekara 58

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Shugaban gwamnonin arewa ta tsakiya kuma gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya taya gwamnan Fulato kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Barr. Simon Bako Lalong murnar cika shekaru hamsin da takwas da haihuwa.
Gwamna Sani Bello a wani sakon taya murnar, ya bayyana Barr. Lalong a matsayin cikakken mutum mai kokarin wanzar da zaman lafiya kuma gimshiki na kwarai.

Ya kara da cewar taya murnar ya biyo fahimtar salon shugabancinsa da nagartarsa.

Sani Bello yace tun bayan shigar shugaban kungiyar gwamnonin arewa ofis solar ga irin salo da gudunmawar da ya bayar, ba a jihar Fulato kawai ba har yankin gaba daya da kasar wanda ya kawo cigaba da fahimtar juna.

Gwamnan yace ” na shiga sahun ‘yan Najeriya dan taya ka murnar cika shekaru hamsin da takwas da haihuwa, ina yabawa salon shugabancin ka da irin gudunmawar da ka ke bayarwa, dan daga martabar arewa da kasa baki daya ba tare da nuna bambamci ba.

” Ina rokon Allah ya kara ma tsawon rayuwa, lafiya da kuma kwarin guiwar cigaba da ayyukan alheri bisa shugabancin ka ga kungiyar mu”.

- Advertisement -