Gwamna Inuwa Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Farfado Da Hanyar Jirgin Kasa Ta Patakwal Zuwa Gombe

0
89

Gwamna Inuwa Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Farfado Da Hanyar Jirgin Kasa Ta Patakwal Zuwa Gombe

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya shaida wa karamar ministar Sufuri Sanata Gbemisola Rukayyat Saraki cewa an yi watsi da hanyar jirgin kasan dake hade yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan da sauran sassan kasar, don haka akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi don farfado da titin jirgin.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi bukatar ce yayin da ya karbi bakwancin karamar Ministar Sufuri a wata ziyara da ta kai masa a gidan gwamnati gabanin kaddamar da makarantar koyar da harkokin Sufurin ta kasa (NITT) reshen Jihar Gombe mai cibiya a Kumo.

Sai ya jaddada bukatar ganin ma’aikatar Sufurin ta Tarayya ta jagoranci farfado da titin jirgin kasa na yankin arewa maso gabas kasancewarsa daya daga cikin muhimman batutuwa ga al’ummar yankin, yana mai cewa gwamnatin sa za ta yi dukkannin mai yiwuwa wajen dafawa makarantar dama sashin sufuri baki daya.

Gwamnan ya ce babu wani nagartaccen shugaban da zai yi watsi da harkar Sufuri saboda muhimmiyar rawar da yake takawa wajen jigilar jama’a da kayayyaki, yana mai bayyana kafa makarantar a Kumo da cewa wani abun maraba ne ga al’ummar Jihar Gombe da Arewa Maso gabas baki daya.

Gwamna Inuwan ya ce makarantar ba kawai matasan shiyyar arewa maso gabas zata amfana ba wajen samun horon sanin makamar sufuri, za ma ta horar dasu su kasance masu dogaro da kai musamman a wannan lokaci da samun aiki ya yi wuya ga wadanda suka yi karatu dama wadanda ba su yi ba.

Ya ce, “A kwanan nan muka samar da wani shafin da zai tattaro mana yawan marassa ayyukan yi, wani abu da ya bani mamaki shi ne mun samu wadanda suka yi rajista da suka kammala jami’a basu da aikin yi dubu four da 752, wasu daga cikin su ma suna zaune ba aiki fiye da shekaru 6, wannan fa na wadanda suka kamala jami’a ne kadai. Kuma 24 daga cikin su masu kyakkyawan sakamako ne mai daraja ta daya. Idan kuma muka hada da wadanda suka kammala karatun diploma da NCE, a kwana gida kadai fiye da mutane 750 ne suka yi rajista, kuma na tabatar ya zuwa yanzu solar kai dubbai.”

To sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa makarantar za ta samar da kyakkyawar dama ga dimbin matasa ta fuskar ayyukan yi a jihar inda za su samu boron da zai amfanar dasu a rayuwa.

Gwamnan ya shaida wa bakuwar tasa cewa gwamnatin sa tana zuba jari sosai a sashin sufuri karkashin shirin ta na samar da hanyiyin mota akalla kilomita 100-100 a kowace karamar hukuma na Jihar, wadda hakan zai hade sassan jihar don sauka ka harkokin sufuri da zirga-zirgan kayayyaki.

Tun farko a jawabinta, Karamar Ministar Sufurin Sanata Gbemisola Rukayyat Saraki ta shaida wa Gwamna Inuwa irin muhimmancin da Jihar Gombe ke da shi ga ci gaban harkokin sufuri a shiyyar, dama irin rawar da makarantar harkokin Sufurin za ta taka wajen samar da kwararrun da ake bukata wajen kyautata ayyuka da nausa sashin na Sufuri gaba ba kawai a Jihar Gombe ba, har ma da shiyyar Arewa Maso Gabas baki daya.

Ministar ta kuma bukaci hadin kai da goyon bayan Gwamnatin Jihar Gombe wajen dafawa ayyuka da shirye-shiryen makarantar, har ma ta nemi alfarman gwamnan kan ya kasance jakadan makarantar a shiyyar arewa maso gabas.

Ta kuma roki gwamnan da sauran takwarorin sa na shiyyar arewa maso gabas, su kimtsa matasan su tare da sanya su a makarantar don samun horon dogaro da kai don rage rashin aikin yi da zaman kashe wando a shiyyar.

Ministar tace Gwamnatin shugaba Buhari tana aiki ba dare ba rana don farfado da sashin tattalin arziki ciki kuwa har da sashin na sufuri, tana mai cewa Gwamnatin Tarayya ta hannun ma’aikatar sufuri tana zuba jari sosai wajen farfado da titunan jirgin kasa cikin har da na Patakwal zuwa Gombe zuwa Maiduguri

Ministar ta kuma mika godiya ga Gwamna Inuwa bisa tallafawa makarantar, tana mai bayyana gwamnatin Gombe a matsayin babbar abokiyar huldar makarantar.

What's On Your Mind?