Gwamna Gombe Zai Tallafa Wa Masana’antu Da Naira Miliyan 500

0
42

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya zai kaddamar da shirin tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da zai lakume kudi Naira Miliyan 500, a matsayin wani mataki na rage illar da annobar Korona ta haifar kan sana’o’i da kamfanoni da suke jihar.

Gwamna Gombe Zai Tallafa Wa Masana’antu Da Naira Miliyan 500Bayanin hakan ya fito ne ta bakin kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki na jihar, Malam Muhammad Gambo Magaji yayin bude shirin bada horo na kwanaki 2 ga masu kanana da matsakaitan masana’antu kan alfanun sabuwar dokar cinikayya ta jihar da kwaskwarimar da aka yi mata don taimakawa ‘yan kasuwan wajen kula da sana’o’i da kasuwancinsu a lokutan matsatsi da ko-ta-kwana.

Ya ce makasudin taron horarwar shine don sanar da masu kanana da matsakaitan masana’antun kan sabin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafa musu, wadanda suka hada da bada kwangilolin da ba su haura Naira Miliyan 50 ba.
Kwamishinan sai ya bukaci mahalarta taron su yi amfani da damar samun horon wajen koyon sabin dokoki da hada-hadar cinikayyar zamani da jihar ta bullo da su don tallafawa harkokin kasuwanci a yayin wannar annoba.

Bambancin Sarakunan Baya Da Na Yanzun – Daga ’Yar Shekara 123

Ya ce “Ina mika sakon fatan alkhairin Gwamna Inuwa Yahaya a gareku, ina kuma shaida muku cewa nan bada jimawa ba gwamnan zai kaddamar da shirin tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da kudi Naira miliyan 500 don tallafa muku ku farfado daga matsalolin da annobar korona ta haifar kan kasuwancinku”.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin kadamar da horaswar dai har da babban mai binciken kudi na jihar Alhaji Umar Bello, da babban sakataren kasafin kudi Jalo Ali, da shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Malam Abubakar Inuwa Tata, da babban Daraktan hukumar cinikayya ta jiha Alhaji Babayola Muhammad, da Daraktan baital malin jiha Aminu Yuguda da sauran kusoshin gwamnati.

Kamfanin Microflex ne ke dawainiyar bada horon, wadda zai gudana a rukunai 2 na mahalarta dari-dari.

What's On Your Mind?