Gwamna Ganduje Ya Amince Da Sauyin Ma’aikata Ga Manyan Sakatarori 4 

0
70

Gwamna Ganduje Ya Amince Da Sauyin Ma’aikata Ga Manyan Sakatarori 4 

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Domin yaba kokarin ma’aikata na daga darajar aiki zuwa babban matsayi don tafiya dai-dai da zamani, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sauya wa wasu manyan sakatarori hudu ma’aikatu tare da nadin sabo guda daya. Kamar yadda babban Daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya Shaida wa MOBILIZED9JA A Yau.

Wannan ci gaba, a cewarsa, “guda ne cikin matakan aiki na yau da kullum. Kamar yadda ake aauyawa manyan ma’aikata wuraren Aiki, daga wannan ma’aikata, sassan Gwamnati da Hukumomi zuwa waccan.”

Daganan sai ya umarci wadanda aka Sauyawa wuraren aikin da su kara Jajircewa kamar yadda ake kyautata masu zaton, gaskiya, sadaukar da kai da kuma kyakkyawan jagoranci wanda zai kara inganta aikin Gwamnati zuwa matakin na gaba.”

Manyan Sakatarorin solar hada da injiniya Muhammad Adamu Musa
daga Hukumar bin ka’i’doji zuwa Hukumar ma’aikata,  Sani Abdullahi Kofar Mata daga Ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma zuwa Ma’aikatar kasafin kudi da tsare tsare, Abba Mustapha Dambatta
daga Ma’aikatar kasafin kudi da tsare tsare zuwa Hukumar bin ka’i’dojin aiki, Salisu M. Gabasawa
daga Hukumar Ma’aikata zuwa Ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma da kuma Amina Muhammad Usman wacce aka tura Ma’aikatar sufuri da gidaje.

Gwamna Ganduje ya hore su da ako da yaushe su ci gaba da amfani da sabbin fasahohin zamani wajen gudanar da ayyukan su. Ya kara da cewa, “Yanzu duniya ta zama a tafin hannu, musamman cigaban fasahohin zamani da kimiyya, iliminku da kuma sabbin fasahohi ako da yaushe ana lale marhabin dasu.”

What's On Your Mind?