Gwamna El-Rufa’i Zai Koyi Da Ganduje Ya Gididdiba Masarautar Zazzau

0
89

Wasu bayanan da MOBILIZED9JA A YAU ta samu a sanyin safiyar jiya Talata na nuna cewa, akwai yiwuwar Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, zai yi koyi da takwaransa na Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya gididdiba Masarautar Zazzau, kamar yadda takwaran nasa na Kano ya yi wa Masarautar Kano.

Idan dai ba a manta ba, Allah ya yi wa Marigayi Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris, rasuwa tun a ranar 20 ga Satumbar wannan shekara, kuma yau kusan kwanaki 16 kenan ba tare da an nada sabon sarki a Masarautar Zazzau ba, wanda hakan ya janyo cece-kuce da suka daga bangarori da dama.

Gwamna El-Rufa’i Zai Koyi Da Ganduje Ya Gididdiba Masarautar Zazzau

Da farko dai masu zaben sarki photo voltaic mika sunayen wadanda su ka zaba, amma a matsayin wadanda za a zabi sabon Sarkin na Zazzau a cikinsu, amma Gwamnan Jihar Kaduna ya ce, bai aminta da sunayen ba sakamakon zargin abinda ya kira na ya gano an bayar da cin hanci da rashawa a yayin gudanar da tantance sunayen wadanda za a zaba din.

Bayanan da ke fitowa a halin yanzu, wadanda har ya zuwa yanzu ba mu tabbatar da sahihancinsu ba, su na nuna cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kammala shirin raba Masarautar Zazzau zuwa gidan sarauta uku kamar haka; Masarautar Kaduna, wacce za ta jagoranci masarautun za a kira da sunan masarautar Turunku, sai kuma Sarkin  Zazzau da Sarkin Kudan.

Shugaban INEC – Gobara Ba Za Ta Shafi Shirinmu Na Zaben Edo Ba

Har a yayin hada wannan rahoto, mu na dakon jiran sanarwa a hukunce daga fadar Gwamnatin Jihar Kaduna.

Sannan duk kokarin da Wakilin MOBILIZED9JA A YAU ya yi, domin jin ta bakin Kwamishinan Kananan hukumomi da Masarautu ta Jihar Kaduna, hakan ya ci turo, domin duk wayoyinsa a kashe su ke.

To, amma MOBILIZED9JA A YAU ta tabbatar da cewa, gwamnan na Kaduna ya kira taron Majalisar Sarakunan Jihar, inda kawo hada wannan rahoton su na can su na ganawa da shi a fadar gwamnatin jihar.

Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Ganduje na Jihar Kano ya raba Masarautar Kano zuwa masarautu hudu bayan samun sabani da Sarkin Kano na wancan lokaci, Malam Muhammadu Sanusi II.

What's On Your Mind?