EndSARS: Gwamna Buni Ya Yaba Wa Matasan Yobe 

- Advertisement -

Gwamna Buni Ya Yaba Wa Matasan Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya yaba da matasan jihar Yobe dangane da mutunta doka da oda ta hanyar kaucewa gudanar da zanga-zangar endsars a jihar, wadda wasu matasa su ka gudanar a fadin kasar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a al’amurran jihar Yobe su ka gudanar a gidan gwamnatin jihar Yobe da ke birnin Damaturu, a ranar Lahadi.

“Wanda hakan matasanmu photo voltaic cancanci yabo na musamman bisa yadda su ka yi amfani da hankali da tunani, inda suka kaucewa gudanar da zanga-zangar EndSars, kuma hakan ya faranta mana rai da alfaharin kasancewar ku masu biyayya.

Gwamna Buni Ya Yaba Wa Matasan Yobe

”Har wala yau, ina mai kara jinjina muku bisa yadda kuka yi wajen gudanar da addu’o’i na musamman domin ganin bayan wannan zanga-zanga da samun cikakken zaman lafiya a Nijeriya baki daya. Wanda hakan ya nuna ku na daban ne,” in ji shi.

A hannu guda, Gwamna Buni ya kara da bayyana cewa gwamnatin sa za ta kara fitar da tsare-tsare da manufofi masu ma’ana wadanda za su kara bunkasa rayuwar matasan jihar Yobe tare da kasancewa abin sha’awa a idanun sauran matasan Nijeriya.

Haka kuma, ya yaba da kokarin da sarakunan gargajiya, shugabanin addini, masu fada a ji a jihar, iyaye da sauran su dangane da yadda a kowane lokaci suke fadakar da al’umma muhimmancin zama lafiya da hakurin zaman tare da juna a duk fadin jihar Yobe.

Sojoji Sun Halaka ’Yan Ta’adda 16 A Borno

A karshe Gwamna Buni ya nuna cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da kokari wajen gina kyakkyawan fahimta da hakuri da juna, tattauna dukan lamuran da suka taso, kana da amfani da ingantattun matakan warware duk wani bambance-bambancen da ke tasowa tsakanin jama’a tare da bunkasa zaman lafiya da hada kai a tsakanin al’ummar jihar.

A nashi jawabi a wajen taron, tsohon mataimakin gwamnan jihar Yobe kuma karamin minista a ma’aikatar ayyuka da gidage, Hon. Abubakar D. Aliyu, ya yaba wa kokarin shugaban kasa Muhammandu Buhari dangane da sauraron koke-koken masu zanga-zangar EndSars.

”Yayin da baya ga hakan, gwamnatin tarayya a shirye take wajen daukar ingantattun matakai domin tunkarar sauran korafe-korafen da masu zanga-zangar suka gabatar.” Ya bayyana.

- Advertisement -