Gwamna Buni Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikatan Yobe

0
142

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya rantsar da sabon shugaban ma’aikatan jihar Yobe, da manyan sakatarori in guda uku, a dakin taron gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu, ranar Laraba.

Gwamna Buni Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikatan Yobe

Sabon shugaban ma’aikatan jihar Yobe, Mohammed Nura tare da sabbin sakatarorin din-din-din; wadanda za su yi aiki a ma’aikatu daban-daban a jihar, wadanda su ka kunshi Abdulkarim Mai Umar, Garba Bilal da Abdullahi Mohammed Daura.

Da yake jawabi ga sabon shugaban ma’aikatan, hadi da sabbin sakatarorin din-din-din, Gwamna Buni ya ce su dauka kan cewa an nada su a wadannan mukaman bisa cancanta, yayin da kuma ya bukace su gudanar da ayyukan su bisa gaskiya tare da aiki dangane da ka’ida da tanadin da dokokin aikin gwamnati suka nuna.

Tirkashi Kalli Abin Mamakin Sarkin Wakar Waka A Wajan Bikin Buhari Bishir Ahmad

Gwamna Mala ya kara da cewa, “Saboda yadda gwamnatin mu take da ingantattun manufofin ci gaban ma’aikatan jihar Yobe, wanda hakan zai kasance cike da fa’ida a tsarin gudanar da gwamnati don ci gaban jihar Yobe.”

Har wala yau kuma, “Kuma ba zamu lamunta da kowane yanayin da zai kawo mana tarnaki ga harkokin gudanar da nauyin da ya hau kanmu, dangane da ci gaban al’ummar mu, a wannan jihar ta mu ba.” In ji shi.

What's On Your Mind?