Gwamna Buni Na Yobe Ya Umarci A Kai Wa ‘Yan Gudun Hijirar Gaidam Tallafi

0
101

Gwamna Buni Na Yobe Ya Umarci A Kai Wa ‘Yan Gudun Hijirar Gaidam Tallafi

Daga Muhammad Maitela,

Babban Sakataren hukumar bayar da tallafin gaggawa a jihar Yobe (SEMA), Dr. Muhammed Goje, ya bayyana cewa, Gwamna Mai Mala Buni ya ba su umurnin shiga lungu da sako tare da daukar kowane matakin da ya dace wajen kai wa yan gudun hijirar Gaidam tallafi a duk inda suke a fadin jihar.

Dr. Goje ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai, a tsakiyar mako jim kadan da kaddamar da raba tallafin gaggawa ga yan gudun hijirar Gaidam, wadanda sukamakon harin Boko Haram suka yi hijira zuwa garuruwan Damaturu, Dapchi, Yusufari, Yunusari,

Nguru, Gashua da makamantan su a jihar.

Boko Haram solar kai farmaki a shalkawatar karamar hukumar Gaidam a jihar ranar jummu’ar da ta gabata wanda hakan ya jawo sama da mutum 7000 kauracewa garin don neman mafaka, al’amarin da ya jawo asarar rayuka da asarar dimbin dukiyar gwamnati da ta jama’a, ta hanyar kone-kone da fasa shagunan yan kasuwa a garin.

A hannu guda kuma, harin ya tsananta tare da jefa jama’ar yankin shiga mawuyacin hali tare da bukatar tallafin gaggawa, wanda gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa ta hanyar hukumar SEMA a jihar wajen saukaka wa talaka halin kunci a lokaci irin wannan. Haka kuma a kokarin ta wajen aiwatar da tallafin cikin gaggawa tare da kai wa ga wadanda abin ya shafa, hukumar ta kafa kakkarfan kwamiti tare da bin yan gudun hijirar duk inda suke.

SEMA a Yobe ta tallafa wa yan gudun hijirar da kayan abinci da na masarufi da shimfido domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta a wannan yanayin, Goje ya ce, “Gwamna Mai Mala Buni, kwana daya da kai harin, ya bamu umurnin daukar kwakkwaran matakin kar mu bar wani dan gudun hijira ya fuskanci matsala.”

“Saboda haka, muna kara bayar da tabbaci kan cewa za mu yi duk abinda ya dace wajen kiyaye mutuncin kowane dan gudun hijira tare da basu muhallan da zasu zauna da jigilarsu zuwa duk garin da suke da bukatar zama; bisa ga zabin su.”

“Har wala yau kuma, ga wadanda basu da zabin garin da zasu tafi, zamu basu zabi da cikakkiyar dama da zabin garin da ya kwanta musu a matsayin inda zasu zauna.”

A hannu guda kuma, dangane da halin da ake ciki, Dr. Goje ya ce da yake mafi yawan yan gudun hijirar suna azumi ne, wanda hakan ya jawo dole a tanadar musu wuraren buda baki, wanda mun tsara gudanar da hakan a cibiyoyi na musamman wanda ya dace dasu.

Mohammed Goje ya kara da cewa, “Sannan kuma mun bayar da muhimmanci ga mata masu juna biyu, kananan yara tare da tsuffi a cikin yan gudun hijirar.” In ji shi.

Kwamared Usman Bin Affan, daya daga cikin masu gudanar da aikin raba kayan tallafi ga yan gudun hijirar Gaidam a karamar hukumar Yusufari, ya ce, “Mun yi rijistar yan gudun hijira sama da 700 a Yusufari. Sannan kuma mun raba musu shinkafa, katon-katon na taliya da indomi, tabarmi, da sauran kayan masarufi a karkashin hukumar SEMA a Yobe.”

What's On Your Mind?