Gwamna Bala Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sha Damarar Bunkasa Tattalin Arziki

- Advertisement -

Gwamna Bala Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sha Damarar Bunkasa Tattalin Arziki

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana takaici yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa tabuka komai dangane da bunkasa tattalin arzikin kasar nan, yana mai cewar, ba abin da gwamnatin take yi face nuna zargin ta akan lamarin.

Ya ce, “Na yi la’akari Gwamnatin Tarayya ta saki hanya dangane da bunkasa tattalin arzikin kasar nan, ana ta zargin juna ne kawai, mukarraban gwamnati ba inda suka fi bajinta face zargi a tsakanin su, ko yaki da cin hanci ma basu aikata katabus akai”.

Gwamnan, wanda yake yin hira da ‘yan jarida ranar Alhamis, jin kadan bayan da ya halarci hawan sallah a kofar Fadan Sarkin Bauchi, ya nuna jaddada bukatar hada hannu na jiga-jigan masu ruwa da tsaki domin farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Da yake nuna muhimmacin bunkasa tattalin arzikin kasa, Gwamnan ya nuna bukatar gwamnatin tarayya ta assasa taron kundumbala na yadda za a samo mafita dangane da matsalolin da suka addabi kasar nan, mai-makon a rika tererensu a kafofin yada labarai.

Ya kuma yi la’akari na gazawar gwamnatin tarayya kan lamuran tsaro a kasar nan, yana mai kira a gareta da ta nemi hadin kan gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomi, hadi da masarautun kasar nan ta yadda za a samo mafiya kan lamuran.

Gwamna Bala ya ce, “Ina fatar za a samu wani yanayi da za a zaman a matakin kasa da zummar yin nazari kan matsalar tsaro ta yadda za a bullo da kwararan matakai na shawo kan matsalar, yana mai nuni da lalle ne a guji maganganu marasa fasali domin kasar nan fa tana dinke ne kuma a cakude”.

Bala har-wa-yau, ya nuna takaicin sa na yadda rashin tsaro daya addabi arewacin kasar nan yake ta watsuwa sauran sassan ta, don haka ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi dukkan mai yiwuwa domin ceta kasar daga rugujewa.

Ya ce, lamarin tsaro baya tattara kan Gwamnatin Tarayya bace ita kadai, har ma da gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomi, hadi da masarautun kasar nan, hasali ma kowa dan sanda ne da ya wajaba ya kawo gudummawa”.

Senator Bala Mohammed sai ya bayyana cewar, “Mun san ko su wanene ‘yan ta’adda, mun kuma san duk wuraren da suke da mafaka da ayyukan su na rashin mutunci, kai wani lokacin ma mune muke daure masu gindi, don haka ya zama wajibi mu zakulo su, domin wannan yaki yafi karfin ‘yan-sanda marasa yawa”.

A yayin Sallar Idin na bana dai, Babban Limamin Bauchi, Imam Ahmad Baban Innah shine ya jagoranci sallar mai raka’a biyu, inda a cikin jawabinsa ya jawo hankalin jama’a da su ji tsoron Allah kana su taimaka wa gwamnati a kokarinta na wanzar da zaman lafiya a jihar, yana mai cewa a ma fadin Afrika, Bauchi na morar zaman lafiya sosai, don haka bai fatan a gurgunta ingancin zaman lafiyan.

Shi ma dai Sarkin Bauchi, Rilwanu Sulaiman Adamu ya gode wa Allah bisa kammala Azumin watan Ramadana da aka yi lafiya, ya kuma jinjina wa kokarin malamai na koyar da al’umma a cikin wa watan Ramadana cikin wa’azozinsu da tafsiransu.

 

- Advertisement -