Gwamna Bagudu Ya Jajanta Wa ‘Yan Sandan Nijeriya Game Da Mutuwar 9 A Kebbi

0
73

Gwamna Bagudu Ya Jajanta Wa ‘Yan Sandan Nijeriya Game Da Mutuwar 9 A Kebbi

Daga: Umar Faruk Birnin-Kebbi

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu a jiya ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa Hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi da ke Birnin-kebbi don jajantawa kwamishinan ‘yan sanda kan rasuwar Babban Jami’in ‘Yan sanda, DPO Abdullahi Jimoh na Sakaba a masarautar Zuru, da  kuma Sufeto Ibrahim Aliyu tare da wasu ‘yan sanda bakwai sakamakon wani harin ‘yan fashi da ya ritsa da su ranar Lahadi.

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya nuna bakin ciki sport da irin wannan aikin ta’addanci da dabbancin da aka yi na kashe jami’an ‘yan sanda wadanda ke kan yi wa kasa aiki don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin da kubuta daga cikin aikin ‘yan fashi da makami.
Ya mika sakon ta’aziyya ga rundunar ‘yan sanda na Nijeriya, iyalan wadanda suka rasun, yana mai bayyana jami’an a matsayin wadanda suka sadaukar da kansu wurin tabbatar da ci gaban kasa a matsayin jarumai, ya kuma roki Allah da ya ba su aljanna da rahamarsa .

Haka kuma Sanatan ya yaba wa dukkanin hukumomin tsaro da ke aiki a cikin jihar bisa ga kwazon su wanda ke samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da goyon bayan da ya dace don bunkasa walwalarsu da kuma kayan aiki da sauran abubuwan da ake bukata don gudanar da aiki yadda ya kamata.

Gwamnan, ya yi alkawarin ware wasu kudade don jana’izar jami’an da aka kasha, sannan ya umarci Mataimakin gwamnan jihar mai ritaya Kanal Sama’ila Yombe Dabai, ya wakilci gwamnati a duk ayyukan da suka shafi kwashe su, jana’izar su da kuma bukatun danginsu.

Haka zalika, Gwamna Bagudu ya gode wa Kwamishinan ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sport da matakin da suka dauka cikin gaggawa kan lamuran da suka shafi tsaro a Jihar Kebbi wanda a ko yaushe suke gudanar da aikin su cikin gaggawa.

A martanin da Sufeto Janar na ‘Yan sandan Nijeriya da Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kebbi, CP Deke Adeyenka Bode (mni) ya wakilta, ya nuna godiya ga gwamnan saboda tausayawa da ya nuna wa Hukumar ’ ‘yan sanda ta kasa da kuma a jihar.

Ya tabbatar da cewa ‘yan sanda a jihar za su ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da yin aiki ga duk wani mai laifi, har sai an samu cikakken zaman lafiya a yankin, yana mai cewa wadanda aka kashe solar mutu a wani aikin da ke mai kama da jihadi, bisa ga hakan mutuwa hanyar da babu makawa ga kowane mutum sai ya dandanata.
Daga karshe ya ce rahotannin solar nuna wasu mambobi biyu na jami’an tsaro na ‘yan sa kai su ma solar rasa rayukansu tare da ‘yan sanda da suka gamu da hari daga wasu ‘yan fashi da makami a garin Makuku a karamar hukumar Sakaba.

What's On Your Mind?