Gwamna Bagudu Ya Bukaci karin Zuba Jari A Sana’ar Kiwon Kifi

- Advertisement -

Gwamna Bagudu Ya Bukaci karin Zuba Jari A Sana’ar Kiwon Kifi

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su kara zuba jari a harkar kiwon kifi domin biyan bukatun al’ummar kasar nan da kuma kara samar da ayyukan yi ga al’umma.

Gwamnan ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya kai ziyarar a gonar kiwon kifi ta Kitari da ke karamar hukumar Bunza a jihar.

Ya ce ziyarar na daya daga cikin kokarin da jihar ke yi na karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu a harkar noma da kuma tabbatar da bunkasa  tattalin arziki Jihar da kuma kasa baki daya.

Haka kuma Bagudu ya ce: “Ziyartar gonar da ke Sabon Gari Jika a karamar Hukumar Bunza da nufin karfafa samar da kifi a manya da kananan sikeli a cikin jihar ta masu zaman kansu.

“Na yi farin ciki da manyan kogunan kifin da na gani a gonar, wanda ke matakin farko na ci gaba, yana da mahimmanci a lura cewa ina cikin farin ciki lokacin da na kewaya.”

Shugaban gonar, Alhaji Abbas Umar-Bunza, ya ce ana kiwon nau’ikan kifaye iri-iri a cikin kududdufin da ka gani a gonar.

Ya nuna gamsuwarsa da irin taimakon da aka samu daga ciki da wajen jihar tun lokacin da ya fara aikin.

Haka kuma Alhaji Umar-Bunza ya ce ya horar da matasa da yawa kan kiwon da kamun kifi wanda daga baya suka zama masu daukar ma’aikata ta hanyar kafa gonakin kifi na kansu.

daya daga cikin masu kula da gonar, Abubakar Ladan, ya ce gonar ta fara ne da tafkunan kifi guda biyar, yayin da ake ci gaba da karin wasu biyar a yanzu.

“An fara aiki a nan shekara guda da ta wuce da tafkunan kifi guda biyar, yanzu haka, ana kan gina wasu karin magudanan ruwa guda biyar domin mayar da su goma.

- Advertisement -