Gurguwa Da Auren Nesa: Bayan Titin Kano-Kaduna-Abuja Ya Gagari Kundila..?

0
51

“Abin dariya wai yaro ya tsinci hakori” kuma Hausawa photo voltaic ce “Abin da wuya gurguwa da auren nesa” bai kamata gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika aikin “Baban-Giwa ba, tana tubka kuma tana warwarewa a arewacin Najeriya. Ina aikin titin Kano Zuwa Kaduna Zuwa Abuja ya kwana?

Daga dukkan alamu gwamnatin Muhammadu Buhari na yin  wasan kura da Mutanen arewa. Dalili kuwa shine ba a kammala titin Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja ba, da titin Kano zuwa Maiduguri da kuma titin Kano zuwa Katsina, sai aka wayi gari da wata sabuwa,ta sake bulla a arewacin kasar nan.

Gurguwa Da Auren Nesa: Bayan Titin Kano-Kaduna-Abuja Ya Gagari Kundila..?

Yau babu tausayi, sai ga sabuwar magana ta sake fitowa sabuwa fil, wanda zai yi wuya gwamnatin Buhari ta iya kammalawa cikin lokacin da ya rage mata.

Abin takaici wai gwamnatin tarayya ta amince da bayar da kwangilar titin jirgin kasa wanda zai  hade da Kano da Dutse da Katsina da Jibiya da kuma Maradi a Jamhuriyar Nijar kan kudi na dala biliyan 1.96.
Gwamnatin tarayya ta amince da haka a taronta na majalisar zantarwa a ranar Laraba 23/9/2020 a fadar shugaban Kasar Nijeriya, wanda ya kai ga amincewa da bayar da kwangilar bayan da ministan sufuri, Rotimi Amechi  ya mika daftarin aiki a wajen taro majalisar zartarwa ta kasa.

Akwai bukatar gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito fili ta yi cikakken bayanin ina aikin hanyar kano zuwa Kaduna zuwa Abuja ya tsaya?, yayin da titin zama tarkon mutuwa, ganin yada gwamnatin Shugaba Buhari ta zuba ido ake yi wa aikin rikon sakaina, wato aikin ya kwangilar yana tafiyar hawainiya. Aikin hanyar hanyar Abuja-Kaduna-Kano, yana  janyo wa gwamnatin Buhari suka musamman daga mutanen Arewacin Najeriya.

KAI KAWAI !!! Yan Boko Haram Da Iyalinsu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji

‘Yan Najeriya suna da masaniyar cewar “gwamnatin Muhammadu Buhari wadda ke kokarin ganin an taimakawa talaka domin samun saukin rayuwa, ya fara fahinta cewar gwamnatin ba da gaske ta ke yi ba. Idan za mu iya tunawa lokacin da aka bayar da kwangilar aikin hanyar Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja akan kudi naira biliyan 155 da miliyan 700, wadda Ministan ayyuka da gidaje da wutar lantarki, na wancan lokaci wato Babatunde Raji Fashola, ya ba da sanarwar bayar da kwangilar.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai tana shan suka musamman daga al’ummar jahohin Kano da kaduna da Katsina da Jigawa da Zamfara da Sokoto kuma su ne  jahohin da suka ba shi kuri’u a zaben da aka yi a shekarar 2015. Sanin kowa ne cewar gwamnatin Najeriya ta ware kudi fiye da naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin gyaran hanyar mai nisan kilomita fiye da 400. Hanyar dai, ta dade da lalacewa al’amarin da kan janyo haduran motoci a wadansu lokuta tare da asarar rayuka.

Amma duk da haka a shekarar 2017 gwamnatin Najeriya ta gyara wani bangare na hanyar wato tsakanin Abuja zuwa Kaduna lokacin da aka rufe filin jirgin saman Abuja domin hanyar jirgi da za a gyara, sai dai saboda da rashin ingantaccen aiki, daga bisani hanyar ta kara komawa gidan jiya.

Akwai tunanin ko  gwamnatin Muhammadu Buhari za ta iya kamla wasu daga cikin manyan ayyukan da ta dauko, ciki har da hanyar da ta taso daga Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja, wadda ta zama aikinta ya gagari Kundila. Kamfanin Julius Berger da aka baiwa aikin akwai alamun ba zai iya kammala aikin titin Abuja zuwa kaduna zuwa Kano ba akan lokaci guda ba, don haka ya akwai bukatar gwamnatiin Muhammadu Buhari ta samo mafita.

Da a ce  gwamnatin Najeriya ta raba aikin titin  tun farko ga wasu ‘yan kwangila da  wa’adin da aka bada aikin da tuni an kare wannan magana. Amma Kamfanin Julius Berger da  ke aikin titin Abuja zuwa garin Kano yana kuma gudanar wasu aiyyukan a sassan Najeriya. ‘Yan Najeriya suna zargin kamfanin Julius Berger na kasar Jamus da yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari karya recreation da yadda aikinsu ya ke tafiya.

A yadda aikin titin Kano zuwa Abuja yake tafiyar hawainiya, babu yadda shugaba Buhari zai tsallake zargin da ‘yan arewa suke yi masa wajen sakaci da kuma yin ko-in-kula da jahohin arewa, duba da yadda ‘Yan majalisar tarayyar Najeriya suka yi kaca-kaca da wannan kamfanin.

Duk da Kamfani ya karbi Naira biliyan 200 kudin so-min-tabi a matsayi Kafin alkalami, da daga hannun gwamnati, aikin da ya ke yi bai yi nisa ba.

‘Yan Najeriya photo voltaic gamsu cewar babu yadda gwamnatin Muhammadu Buhari za ta iya kammala aikin titin Abuja zuwa Kano akan lokaci. Idan kuwa gwamnati da gaske ta ke, akwai bukatar rarrab aikin titin ga wasu ‘yan kwangila. Saboda haka ya kamata gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbe aikin tare da   rabawa wasu  kamfanonin, domin Kamfanin Julius Berger ka dai ba zai iya kammala aikin kwangilar titin ba.

Hakika Mutanen Najeriya photo voltaic cikin damuwa, dangane da yadda aikin gyaran titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano ke tafiyar-hawainiya, ko tafiyar-kunkuru. Idan zamu
tun cikin shekara ta 2018 aka bayar da kwangilar aikin, amma ga shi har 2020 ta kusa shuɗewa, ba a yi nisa da aikin ba. A gaskiya  kamfanin dake aikin gina titin wato Julius Berger ya ba ‘yan Najeriya kunya, tare muzanta gwamnatin tarayya, ganin yadda aka shafe tsawon  shekaru sama da biyu ko shekaru uku  aikin da ya ki ci gaba.

A zahirin gaskiya akwai bukatar ko dai a kwace aikin ko kuma a  rarraba aikin titin mai tsawon kilomita 400 ga wasu kamfanoni, domin su taya Julius Berger kammala aikin da sauri, Kuma akan lokaci.
Babu wani mutumin Najeriya da ya ji  dadin yadda  aikin titin ya shafe  sama da shekaru uku  da suka gabata, amma a ce har yau aikin da aka yi bai kai kashi 40 cikin 100 ba. Duk da cewa Kamfanin ya karbi  biliyoyin nairori daga cikin biliyan  155.7 na yawan kudin kwangilar, amma  har yanzu ba su yi abin kirki ba. Ku na da masaniya gwamnatin Muhammadu Buhari da Kamfanin Juli photo voltaic yi yarjejeniyar cewa za a kammala aikin titin cikin watanni 36 da suka diba, suka ce a cikin su za su kammala aikin gaba daya.

Idan muka dubi bangaren farko na aikin titin daga Zuba zuwa Kaduna, abin haushi da takaici, sai dai Mutanen Najeriya su yi hakuri,  amma fa aikin na cike da kurakurai, domin nisan titin kilomita 165 ne daga Zuba zuwa Kaduna.
Gyaran da a ka yi daga Kaduna zuwa Zaria babu yabo babu fallasa, ko  Kuma daga Zaria zuwa Kaduna sai dai abar Kaza cikin gashinta.

Amma ‘yan Najeriya ya kamata su fahinci cewar Kamfanin na Juluies Berger na da uwa a gidin Murhu a cikin  kunshin gwamnatin Muhammadu Buhari, idan ba haka, da tuni an kwace aikin, saboda haka dole kamfanin ya ci karensa babu babbaka.

Saboda rashin kammala aikin da wuri sai asarar rayuka da dukiyoyi ake ta yi ba kakkautawa a kan titin.
Babu wani dalili da ‘yan Najeriya ba za su koka da irin yadda aikin ke tafiya ba, haka ya fito fili ganin yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza daukar mataki akan Kamfanin har ya kammala zangon mulkinsa na farko, kuma idan ba a yi hankali ba, zai  kammala zangon sa na biyu.

Kai wannan matsala ba a titin Kano zuwa Abuja matsalar ta tsaya ba, ina aikin titin Kano zuwa Maiduguri yake, aikin ya ki ci, ya ki cinyewa, tsawon shekaru 13 ke nan.

Gaskiya dole duk mutumin arewa ya nuna matukar damuwa dangane da yadda aikin gyaran titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano ke tafiyar-hawainiya, ko tafiyar-kunkuru.

Amma idan shugaban Kasa muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa titin Kano zuwa zariya zuwa Kaduna zuwa Abuja ba a kammala shi ba, ‘Yan arewa za su shiga cikin takaici.”

What's On Your Mind?