Gobe Za A Kaddamar Da Littafin Diwanin Wakokin Aminu Ala A Kano

- Advertisement -

Gobe Za A Kaddamar Da Littafin Diwanin Wakokin Aminu Ala A Kano

Daga Saddik Muhammad A Kano

Idan Allah ya kai mu gobe Asabar 22/5/2021, za a yi taron kaddamar da littafin DIWANIN WAKOKIN AMINU ALA, wanda ya kawo tarihi da wakoki da kuma Gwagwarmayar rayuwar fitaccen Mawaki Dr. Aminu Ladan Abubakar (Ala).

Kamar yadda Kwamatin kaddamar da littafin ya sanar wa manema labarai, za a kaddamar da littafin ne a gobe asabar a babban dakin taro na Musa Abdullahi Corridor da ke Sabuwar Jami’ar Bayero da misalin karfe 10-30 na secure.

A sanarwar da Kwamatin kaddamarwar ya fitar ta bayyana cewar manyan baki daga garuruwa daban daban na kasar nan da ma kasashen makota ne za su halarci wajen wannan taron da zai kasance a karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da kuma Mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji (Dakta) Nuhu Muhammad Sunusi.

Manyan bakin da za su gabatar da littafin su ne AMBS Gen T Y Buratai da AMBS Acht Aminu Dabo. tare da AGF Ahmad Idris da kuma Dakta Bukar Usman. Yayin da Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, Alhaji Dattijo Hamma, Alhaji Samsudden MD Yusuf, Alhaji Sulaiman Sa’id Zaria da Alhaji Ibrahim Jalo za su rufa musu baya.
Babban Malami Farfesa Isah Mukhtar shi ne mai bitar littafin ya yin da Dakta Ibrahim Satatima zai kasance mai gabatarwa a wajen taron.

Marubutan littafin dai Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Abu-Ubaida Sani masana ne a kan harkar Adabin Hausa da kuma tarihi da suke koyarwar da Hausa a Jami’ar Danfodiyo da ke Sokoto, kuma solar yi rubutu babu adadin a kan abin da ya shafi tarihi da kuma al’adun Hausa. Don haka ba Sabbin shiga ba ne a kan rubutu wannan ya sa ma a ke ganin sabon littafin nan da suka yi hadaka wajen rubuta shi zai bayar da ma’anar da ta dace a fagen ilimi da kuma tattara bayanai da suka shafi Adabin Hausa.

 

- Advertisement -