Gobara ta kashe mutum 134 a Kano a 2020

0
42

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce mutum 134 ne suka rasa rayukansu a 2020 sakamakon gobara 786 da suka tashi a wuri daban-daban a jihar.

Amarya ta rasa budurcin ta wajen neman kudin yin “event” din auren ta

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Saidu Muhammad, mai magana da yawun hukumar, yana bayyana cewa kazalika an rasa dukiyar da ta kai naira miliyan 635 a tsawon shekarar.

Gobara ta kashe mutum 134 a Kano a 2020

Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.Haka nan, hukumar ta ceto ran mutum 1,077 da kuma dukiya naira biliyan 2.56.

“Akasarin gobarar solar faru ne sakamakon ganganci wurin aiki da tukunyar fuel da amfani da wayoyin lantarki marasa inganci,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta ƙara horas da ma’aikatanta guda 350 a 2021 domin kyautata aiki kuma ya shawarci magidanta da “su riƙa kulawa da kyau yayin amfani da wuta” domin guje wa tashin gobara.

What's On Your Mind?