Shugaban INEC – Gobara Ba Za Ta Shafi Shirinmu Na Zaben Edo Ba

0
49

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta gama duk wani shiri don  gudanar da zaben gwamna da za a yi a Jihar Ondo a ranar Asabar mai zuwa, 10 ga Oktoba, 2020.

Farfesa Yakubu ya ce, “Hukumar ta shirya wa zaben. Yau kwana na biyu a nan Jihar Ondo ina duba shirye-shiryen da mu ka yi kuma na gamsu da abin da na gani.”

Shugaban ya bada wanban tabbacin ne a wajen wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki  a wani babban zauren taro da ake kira Dome Worldwide Custom and Ebent Centre a birnin Akure a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2020.

Ya yi wannan bugun kirjin ne duk da yake an yi wata gobara wadda ta lakume injinan karanta katin zabe kamar yadda aka fada a labarai kwanan nan.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa,  “Sport da gobarar nan abin bakin ciki da ta faru wadda a watan jiya ta cinye dukkan injinan mu na karanta katin zabe a Jihar Ondo,  mun kawo isassun madadin su daga Jihar Oyo kuma mun sake saita su don zaben da za a yi ran Asabar. Mun yi isasshen shiri tare da Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Kasa don tabbatar da cewa irin wannan abu bai kara faruwa ba.”

Gobara Ba Za Ta Shafi Shirinmu Na Zaben Edo Ba

Yayin da ya ke lisaafa irin natakan da aka dauka don samun gudanar da zaben ranar Asabar cikin nasara, Farfesa Yakubu ya ce, “Mun dauki dukkan ire-iren ma’aikatan wucin gadi da mu ke bukata, mun horas da su, mun tantance su, saboda zaben. Mun kai kayan aiki marasa hatsari zuwa dukkan Kananan Hukumomi guda 18 na Jihar Ondo. Mun gargadi ma’aikan mu (na wucin gadi da na dindindin) da su yi aiki na kwararru kuma ba tare da wariya ba wajen gudanar da ayyukan da aka dora masu. Ana ci gaba da aikin wayar da kai da fadakar da masu zabe. Mun gama shirin kwasar ma’aikata da kayan aiki zuwa wuraren zabe a dukkan rumfuna 3,009 da mazabu 203 da ke fadin jihar. Yau da yamma, Babban Bankin Nijeriya zai kai dukkan kayan aiki masu hatsari zuwa reshen sa na Akure. Sport da gobarar nan abin bakin ciki da ta faru wadda a watan jiya ta cinye dukkan injinan mu na karanta katin zabe a Jihar Ondo,  mun kawo isassun madadin su daga Jihar Oyo kuma mun sake saita su don zaben da za a yi ran Asabar. Mun yi isasshen shiri tare da Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Kasa don tabbatar da cewa irin wannan abu bai kara faruwa ba.

“Mu na ci gaba da aiki kafada da kafada tare da hukumomin tsaro a karkashin Kwamitin Tuntubar Hukumomi kan Tsaro a Zaben (Inter-Firm Consultatibe Committee on Election Security, ICCES) don tabbatar da yin zaben cikin kwanciyar hankali da tsaro a ranar 10 ga Oktoba.

“Ina so in yi godiya ta musamnan ga dukkan hukumomin da ke cikin ICCES, musamman jagorar hukumomin, wato rundunar ‘Yansandan Nijeriya, saboda yadda su ke ci gaba da bada goyon baya da aiki cikin kwarewa a lokacin da mu ke shirin zaben.

“A takaice, Hukumar ta shirya wa zaben. Yau kwana na biyu a nan Jihar Ondo ina duba shirye-shiryen da mu ka yi kuma na gamsu da abin da na gani.”

Kalli Abun Takaici Ma’aurata Abinda sukayi Kafin Suyi Aure Boye Wani Mai Wa’azi

Shugaban na INEC ya kuma fadi cewa: “Tun daga lokacin da Hukumar ta fitar da jadawalin ce the ranaku da ayyukan zaben gwamna na Jihar Ondo watanni takwas da su ka gabata a ranar 6 ga Fabrairu, 2020, mun yi ta aiki tare da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su a wajen tarurrika daban-daban. Kuma mun yi ta musayar ra’ayoyi da hukumomin tsaro a matakin kasa da na jiha. Mun yi tuntuba da, tare da neman goyon baya da addu’ar Majalisar Sarakuna ta Jihar Ondo. Mun zauna da shugabannin addini, kungiyoyi masu zaman kan su da kuma kafofin yada labarai. Mun tattauna da Kwamitin Wanzar da Lumana na Kasa (Nationwide Peace Committee) da ke karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami A. Abubakar, GCFR, wanda ya gayyato jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su za su zauna su rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya a nan Akure gobe.”

Farfesa Yakubu ya ce, “Babban burin mu shi ne mu tabbatar da cewa zabar wanda zai zama Gwamnan Jihar Ondo gabadaya ya na hannun masu zabe.

“Ina so in tabbatar wa da dukkan masu zabe cewa kowace kuri’a da za a kada za ta yi tasiri kuma wanda jama’ar Jihar Ondo su ka zaba kadai ne zai kasance sakamakon zaben.

“Ina so in tabbatar wa da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su cewa za mu ci gaba da kasancewa masu alkibla kan dokoki da ka’idojin aikin mu. Bari in kara tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki cewa Hukumar Zabe ba za ta dauki kowane irin mataki don ta dadada ko bakanta wa wata jam’iyyar zabe ko dan takara ba.

“Hukumar ta yi nazarin yadda ta gudanar da zaben gwamna kwanan nan a Jihar Edo. A shirya mu ke mu ci gaba da inganta aikin mu. Saboda wannan dalilin, mun gano wurare 16 da ke bukatar inganta aiki, wadanda su ka hada da kayan aiki, daukar mataki kan injin zaben da ya samu matsala cikin gaggawa a Ranar Zabe, matsalar sayen kuri’a a lokacin zabe, da kuma bin dokokin kare kai daga cutar korona. Don haka, mun dauki hayar masu motoci da jiragen ruwa na sufuri don kai da kawon kayan aiki a wurare masu tsandauri da kuma wadanda ke yankunan da ruwa ya ke.

“Mun kara daukar ma’aikata guda 104 aiki don bada tallafi a yankunan da masu zabe su ka yi rajista don su yi aikin gaggawa kan injinan karanta kati a Ranar Zabe.”

What's On Your Mind?