Girmamawa yana Dauke – Kalmomin Girmamawa

0
43

Kalmomin Girmamawa

A makonnin biyu da suka shude, mun ga nau’ukan kamalai da dama. Wadanda ire-irensu ne suka fi cancantar su rika yawo a tsakanin ma’aurata, idan har da gaske suna burin karfafar zamantakewar tasu ne, yadda za ta iya kai wa da tudun mun tsira. A wannan mako kuma za mu dora da kalaman girmamawa.

Daga mafiya muhimmancin abubuwan da ma’aurata suka kamata su sani sport da sadarwa tsakaninsu, akwai yin amfani da kalmomin girmamawa, maimakon na umarni. Wato, mu fahimta cewa yayin da muke neman wani abu daga abokan zamanmu, kalmomin rara-gefe ne su ka fi dacewa da mu.

Rara-gefe a nan yana nufin yin magana cikin wani salo, ta yadda wanda ka ke yi wa maganar in ya ji zai iya fahimtar abin da kake so. Wannan yanayin kuma shi ne yanayin da ya fi dacewa da ma’aurata.

Kalmomin Girmamawa

Tacewar wannan nau’in kalamin a bayyane yake, idan muka yi la’akari da yadda kalaman umarni yake kankantar da wanda ake yi wa. Tsakanin dai miji da mata wata girmama ce ta musamman, wadda kowannensu ya cancanci ya yi dayan. Sabanin dangantakar da take tsakanin ‘ya da mahaifi. Idan uba zai yi magana da ‘yarsa karama ne kai tsaye sai ya ce, “Tashi ki dauko min ruwan sha.”

A wurin yara,wannan nau’in umarnin daidai ne, kuma dama irin sa suke tsammanin ji. Amma a wurin babba, tare da cewa ba saba ka’ida ya yi ba, bas hey suka fi dadin ji ba. Shi kuwa girmama juna da yin dukkan abin da abokin zamanka zai ji yana da muhimmanci a wurinka, shi ne abin budewa kofa, don kyautata zamantakewarmu.

Mu dubi wannan misalai: Idan Maigida ya ce. “Kin kuwa tuna irin kunun ayar nan da kika yi mana ranar sallah? Kai wannan kunu da dadi yake, har yanzu ban dena marmarin sa ba.” Daga jin sa Uwargida ta san yana sanar da ita ne cewa yana bukatar irin wannan kunun.

Don haka tun daga lokacin za ta fara tunanin yaushe za ta samar da shi. Kuma za ta yi dukkan ayyuka da dawainiyar neman kayan harhada shi cikin nishadi ne. Hannu guda kuma, idan Maigida ya ce. “Rabon da a yi min kunun aya a gidan nan tun ranar sallah, watakila kuma sai bayan shekaru goma a kara yi.” Shi ma daga ji Uwargidan ta san so yake ya nuna bukatuwarsa ga kunun ayar.

Sai dai tare da cewa maganganun biyu da manufa daya aka yi su, sigarsu ta sha bamban.

Kuma, mai magana ta farko, ya fi kama da maganar manya akilai, yayin da mai magana ta biyu ya fi kama da yara matasa, a lokacin da suke ganiyar kuruciyarsu. Haka nan, yayin da magana ta barko take bayuwa ga nuna girmamawa da soyayya da kusantuwa ga bunkasa fahimtar juna tsakanin ma’auratan. Ta biyun kuwa ta fi kama da nuna izza da kaskantar da sashe, sannan ba ta bayuwa ga samar da fahimta a tsakanin abokan zama.

Karanta: Karin Farashin Fetur Da Lantarki: Yau ’Yan Kwadago Ke Bijire Wa Umarnin Kotu

Harwayau, akwai bambanci tsakanin kalaman matar da za ta ce wa Maigidanta. “Ina ma dai za ka samu lokaci a wannan satin ka share kwatar nan.” Da wadda za ta ce. “Idan fa b aka share kwatar nan ba za ta iya rusha katangar nan. Duk ta cushe fa, ruwan ba ya tafiya.” Domin a lafazin mata ta farko rara-gefe ne, wanda kuma kai tsaye yake bayuwa zuwa ga so da karfafa gwiwa. Yayin da mata ta biyu ta yi amfani da wani dan karamin gatsali, wanda sam ba ya bayuwa ga so. Ba kuma ya karfafar gwiwar magidanta, sai dai yak o ya ingiza su zuwa ga tirjiya.

Abu ne mai matukar kyau mu fahimci cewa, ba laifi ba ne mutum ya yi wa abokin zamansa umarni a cikin wani abu da zai taimake su, ko wani sashe nasu. Musamman ma miji ya yi wa matarsa umarni. Amma a lokaci guda kuma ya kamata mu sani cewa, abu mafi muhimmanci shi ne mu yi dukkan wata hulda tsakaninmu da abokan zamanmu ta irin sigogin da za su ji cewa suna da wani matsayi ko daraja ta musamman a wurinmu.

Misali, yayin da ka nemi abu a wurin aboki ko abokiyar zamanka ta sigar rara-gefe, kamar kana nuna mata ne cewa tana da wani abu wanda idan ta yi zai faranta maka, ko kuma zai taimake ku gaba daya. Kuma wannan abin ba dole ba ne. don haka in ma ta tashi yi za ta dauka a ranta cewa kamar taimako ko kyautatawa take yi. Saboda haka, sai aikin ya zama mafi nishadi a wurinta.

Domin dukkanmu muna sane da cewa ayyukan da muka yi don sa kai ko kyautatawa photo voltaic fi mana sauki da nishadi yayin aiwatar da su fiye da wadanda muke yi da suka zame mana dole. Amma yayin da ka yi wa abokiyar zamanka umarni, maimakon rara-gefen. Kana bayyana kanka a matsayin oga ne kawai, wanda yake da cikakken iko, wanda kuma idan ya bayar da umarni dole ne a bi kawai.

Ita kuma soyayya, magana ce ta zabi. Kamar yadda ya zabe ki, ko kika zabe shi, to kamata ya yi kusan komai naku har yanzu ya zama akwai damar zabi. Mutumin da ya yi rara-gefe yayin da yake neman wani abu daga wurin abokin zamansa, tamkar yana ba shi zabi ne.

Zai iya yarda, ko kuma shi ma ya kawo nasa hangen a cikin wannan sha’ani din. Sabanin wanda zai bayar da umarni, wanda shi kawai aiwatarwa yake bukata babu kofar zabi ko bayyana hangen dayan a ciki. Do duk inda kuwa aka samu wadannan yanayi biyu, z aka taras wancan mai rara-gefen shi ne yake da tafiya a kan ka’idoji na soyayya, amma wancan mai umarnin tuni ya sauka.

Don haka idan an ga soyayya ta yi saurin harhade komatsanta ta yi hijira daga irin wannan gidan ba wani abin mamaki ba ne. Korar ta aka yi ta karfi da yaji.

Yi tunani, a matsayinka na magidanci, idan har kana so ka fahimci cewa da gaske ne matarka son ka take yi. Sai ka ba ta wata dama wadda za ta ji ra’ayinta ne ta nuna maka kulawa, ta bayyana yadda kake birge ta, ta kayutata kalamanta yayin ganawa da kai, kuma ta shagaltu a cikin yin abubuwan da ta tabbatar suna kayatar da kai. Irin wannan yanayin ne da zarar ka equivalent shi za ka gamsu a ranka cewa da gaske ne son ka ake yi. Amma a hannu guda, idan ya zamana komai da kake so daga wurin matarka kana samun sa ne ta hanyar yi mata umarni, sai mu ce zamanku ya fi kama da na Baiwa da Ubangidanta.

Wato hidimdumu ne da ake yin su saboda tsoro da fargabar matsalar da za a fuskanta in an gaza samar da su. Amma ba don dadin rai ko zabi ba. Ka ga kenan, tuni an yi watsi da wncan tsarin da tun farko ake gina soyayyar a kansa.
Nan za mu dakata, sai kuma mako na gaba in Allahu mabuwayi Ya sahale ma na, za mu zo mu dubi gaba ta gaba, in sha Allahu.

What's On Your Mind?