An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa

0
110

Akalla mata sojoji 300 rundunar soji ta girke don magace ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane, a babban titin Kaduna-Abuja, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya karbi 100 daga cikin sojoji mata 300 ranar Laraba.

Da yake bayani ga sojojin, El-Rufai ya bayyana kwarin gwiwar cewa girke jami’an mata akan babban titin zai kawo karshen rashin tsaro a hanyar.

Da yake bayani ga sojojin, El-Rufai ya bayyana kwarin gwiwar cewa girke jami’an mata akan babban titin zai kawo karshen rashin tsaro a hanyar.

Akalla mata sojoji 300 rundunar soji ta girke don magace ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane, a babban titin Kaduna-Abuja, The Punch ta ruwaito.  Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya karbi 100 daga cikin sojoji mata 300 ranar Laraba.

Gwamnan ya bukaci rundunar soji da ta girke karin jami’ai don karawa sojojin da ke aiki a hanyar karfi don shawo kan garkuwa da mutane a babban titin.

Gwamnan ya ce, “matsalar titin Abuja-Kaduna za ta zo karshe da saboda girke jami’a mata saboda abin da namiji zai yi mace zata iya yin fiye da shi. Mun yadda da ingancin mata a wannan jihar.

Abubuwa biyar da Buhari ya gaya wa sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya

“Ina da yakinin titin zai zama mafi tsaro a Najeriya. Za muyi duk mai yiwuwa don ganin an samu nasarar aikin. Ganin ku zai janyo mata da yawa shiga aikin soja. Shiyasa muke da mace mataimakiyar gwamna don karfafawa wasu matan gwiwa.”

Babban kwamandan runduna ta daya, Kaduna, Manjo Janar Usman Mohammed, ya nuna irin jin dadin sa da yadda gwamnatin jihar ke bawa sojoji da sauran jami’an tsaro gudummawa.

Mohammed ya yabawa gwamna El-Rufai da mataimakiyar sa, Dr Hadiza Balarabe, kan yadda suka karbi jami’an da kan su

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Instances ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami’in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

What's On Your Mind?