Gaskiyar Zance ! Mene ne ke faruwa tsakanin Aminu Saira da Arewa24 kan Labarina?

0
42

Tun bayan da aka kammala nuna zango ba biyu na fim ɗin Labarina mai dogon zongo, na kuma yi rubuta a shafina na Fb cewa za mu sanar da lokacin da za a ci gaba da nuna zango na uku da kuma tashar da za a nuna, mutane da dama ke yin sharhi a kan lamarin daidai gwargwadon fahimtarsu.

Sai dai abin da ya fi shahara a bakunan mutane har ma da wasu kafofin watsa labarai shi ne kamfanin Saira Motion pictures ya samu matsala da gidan talabijin din Arewa24 masu nuna Labarina, wasu ma har cewa suke yi ba za a ƙara nuna fim ɗin a tashar ta Arewa24 ba.

Tun daga lokacin muke samun tambayoyi da dama ni da abokan aikina a Saira Motion pictures kan gaskiyar lamarin da kuma jita-jitar da ake yaɗawa.

Kuma hatta wasu ma’aikatan tashar Arewa24 solar tambaye ni wai me ke faruwa ne?

Ta wata fuskar lamarin ya kan ba ni mamaki, musamman ganin yadda jama’a suke kitsa labarin ƙala-ƙato su ringa yaɗa shi bayan solar san ƙarya suke yi.

A wasu lokutan kuma ba na mamaki, domin hakan na nuna irin karɓuwar da shirin na Labarina ya samu a wajen masu kallo da kuma irin zumuɗin da suke yi na ganin ci gabansa.

To amma a wani lokacin na kan yi takaici ganin cewa wasu kafofin watsa labarai na shiga cikin wannan yuyumar ta yaɗa labaran ƙanzon kurege, su yaɗa abinda ba su da tabbas a kai, kawai don solar ga mutane na magana a kai. Tabbas irin waɗannan solar ci amanar aikin jarida.

Gaskiyar Lamari

Na yanke hukuncin yin wannan rubutu ne a BBC bayan tashar ta tuntuɓe ni don jin haƙiƙanin abinda ke faruwa da kuma jin gaskiyar lamari, tamkar dai sunan wani shiri na tashar ta BBC Daga Bakin Mai Ita.

Zance na gaskiya shi ne, mun shiga yarjejeniya da tashar Arewa24 don nuna fim ɗin na Labarina mai dogon zango wanda kamfanin Saira moveis ne yake da haƙƙin mallakarsa.

Yanzu Yanzu- Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Ya Gwangwajewa Jarumin Tijjani Asase Da Kyautar Sabuwar Mota

Kamar yadda ake irin wannan yarjrjeniya a ko ina a duniya, mun amince cewa ba za mu bai wa kowa fim ɗin zango na ɗaya da na biyu ba tsawon shekaru biyu, ita kuma tashar ta Arewa24 za ta ringa nuna shi ne a talabijin da kuma sanya shi a manhajar Arewa24 on Demand.

Idan mu da Arewa muna buƙatar sabunta yarjejeniyar bayan shekara biyu za mu iya sake ƙulla wata, idan kuma ba ma bukata to shi kenan, magana ta kare.

A yanzu haka dai ba a naɗi zango na uku da na huɗu na fim ɗin Labarina ba, don haka babu wata yarjrjeniya tsakaninmu da kowa kan sabbin zangon da za a ɗauka.

Kuma ko da ita tashar ta Arewa24 ba mu da wata yarjejeniya ko wata magana kan fim din, tun da ba za a yi maganar abin da babu shi a ƙasa ba.

Ba za mu yi maganar inda za a nuna ci gaban shirin ba har sai mun kammala ɗaukarsa, muka kuma kammala aiki a kansa.

Gaskiyar Zance ! Mene ne ke faruwa tsakanin Aminu Saira da Arewa24 kan Labarina?

A lokacin ne za mu iya shiga yarjejeniya da duk waɗanda suka ga ya burge su kuma ya kai irin mizanin da suka ajiye kafin su nuna wani shiri a kafarsu.

Sannan idan mun yi magana da su muka fahimci juna, sai mu sanar da jama’a cewa ga inda za a kalli sabon shirin.

Amma hakan ba ya nuna cewa mun samu wata matsala da tashar Arewa24 ko kuma ba za a ƙara nuna fin ɗin a tashar ba.

A iya sanina a matsayina na mai shiryawa da ba da umarnin shirin ban san muna da wani saɓani da Arewa24 ba, ko kuma rashin jin daɗin mu’amalar da muka yi a baya ba.

Zan iya bugar kirji in ce dukkanmu mun ji daɗin mu’amala da juna kuma ma zan iya cewa babu abinda zai hana mu sake kulla alaƙa nan gaba idan dukkanmu mun amince da sharaɗan da za mu gabatawa juna.

Yaushe za a fara nuna ci gaban shirin Labarina?

Kawo yanzu dai ba mu sa rana ko lokacin da za a fara nuna ci gaban Labarina ba, domin kuwa har yanzu ba mu fara naɗarsa ba.

Amma dai nan da makwanni biyu masu zuwa muke sa ran fara naɗar sabon shirin, kuma sai mun yi wata guda muna naɗarsa sannan za mu iya samun haske kan yaushe za mu iya samar da fim ɗin na adadin makwannin da za mu iya fara nunawa.

Amma dai duk da haka muna tabbatarwa da masu kallo cewa za ku ji daɗin sabon shirin na Labarina, musamman ganin irin karɓuwar da ya samu a wajenku, kuma muna tabbatar muku cewa za mu yi kokari mu fara kawo muku shi ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba.

Mun dauko muku wannan rubutu daga bbchausa

What's On Your Mind?