Gargadin Buhari Ga Akeredolu: Kada Ka Ci Amanar Mutanenka

0
62

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin zababben Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a kan ya tsayu da daukan amanar da mutanan Jihar suka danka masa ba tare da ya ci amanarsu ba, ta hanyar yi masu kyawawan ayyuka sama da wadanda ya yi masu a zangonsa na farko.

Shugaban kasan ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa wacce mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin manema labarai da wayar da kai, Mista Femi Adesina, ya fitar, haka nan shugaban kasan ya yaba wa al’ummar na Jihar Ondo a bisa yaDda su ka nuna dattako a lokacin zaben gwamnan Jihar da ya gabata a ranar Asabar a inda su ka gudanar da zaben lami lafiya.

Gargadin Buhari Ga Akeredolu: Kada Ka Ci Amanar Mutanenka

Ya kuma yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC), da sauran hukumomin tsaro a bisa rawar da su ka taka a lokacin zaben har komai ya tafi sumul kalau.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana taya Rotimi Akeredolu SAN, murna a zabensa da aka sake yi a karo na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Ondo na tsawon wasu shekarun hudu.

Ambaliyar Hadeja Kaddara Ce Daga Allah – Salisu Birniwa

Ya gode wa al’ummar Jihar Ondo a bisa yadda suka mara wa gwamnan da Jam’iyyar APC baya, ya yi nuni da cewa mutane su na da cikakkiyar masaniyar ko wane ne Gwamnan da kuma jam’iyyar ta APC, wadanda suka yi masu gagarumin aiki tukuru a cikin Jihar.

“Shugaban kasan ya bukaci Gwamnan ya kasance mai yawan hakuri da godiya a bisa gagarumar nasarar da Allah ya ba shi.

What's On Your Mind?