Ganduje Ya Zabtare Rabin Albashin Masu Rike Da Mukaman Siyasa

0
97

Ganduje Ya Zabtare Rabin Albashin Masu Rike Da Mukaman Siyasa

Gwamnatin Jihar Kano ta zabtare albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 100 na watan Maris, sakamakon raguwar kudaden shiga da da Jihar take samu.

WAEC Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 215,149

Kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, shi ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne bayan karancin kasafin kudaden da jihar ke samu daga asusun gwamnatin tarayya. Ya kara da cewa, matakin zai shafi gwamna da mataimakinsa da sauran masu rike da mukaman siyasa da ke fadin jihar ciki har da kwamishinoninsa da masu bada shawara na musamman da mataimaka da dai sauransu. Garba ya ce, a matakin kananan hukumomin zabtarewar albashin ta shafi shuwagabannin kananan hukumomi da mataimakinsa da kansiloli da sakatarori da masu bada shawarwari.

Ganduje ya zabtare rabin albashinsa da na sauran masu rike da mukaman siyasa ne bayan da jihar take fuskantar raguwar shamun kudaden shiga a duk wata.

What's On Your Mind?