Ganduje Ya Mika Sakon Ta’aziyya Ga Sarkin Kano Da Na Bichi Bisa Rasuwar Mahaifiyarsu

0
78

Ganduje Ya Mika Sakon Ta’aziyya Ga Sarkin Kano Da Na Bichi Bisa Rasuwar Mahaifiyarsu

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana rasuwar Hajiya Maryam, mai babban daki, kuma mai dakin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da cewa kaddarace wacce kowa sai ya danda neta, yace, amma dai duk da haka Jama’ar Kano zasu ci gaba da tuna kyawawan ayyukan alhairin ta.

Gwamnan wanda ya girgiza kwarai da jin labarin wannan rasuwa, “amadadin Gwamnati da al’ummar Jihar Kano muna mika sakon ta’aziyya ga iyalanta, Sarkin Kano dana Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Cikin kunshin sakon ta’aziyyar da Kwamishinan Ma’aikatar yada labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya gabatar,  Gwamna Ganduje ya ci gaba da bayyana marigayiyar a matsayin mai gaskiya, da’a, uwa wacce ta tarbiyantar da yaranta hanyar Allah, don haka sai ya bukaci Sarakunan biyu dasu nuna juriyar wannan babban rashi, musamman ganin yadda mahaifiyar tasu ta tafiyar da rayuwar ta wajen bautawa Allah.

Ganduje yace,  mutuwarta a wannan lokaci ta bar wagegen gibi mai wahalar cikewa, musamman ga yaran nata biyu wadanda ke matukar bukatar kulawarta da nuna masu yadda abubuwan da ya kamata suyi.

Gwamnan ya kuma yi addu’ar fatan Allah ya kyautata makwancinta da na Marigayi Sarkin Kano, yasa suna Aljannar fiddausi, ya roki daukacin al’ummar Jihar Kano da Masarautu nan biyu da cewa Allah ya basu karfin halin jure wannan babban Rashi.

What's On Your Mind?