Ganduje Ya Kaddamar Da Kwamitin Tsara Dabarun Yaki Da Cin Hanci A Jihar Kano

0
99

Ganduje Ya Kaddamar Da Kwamitin Tsara Dabarun Yaki Da Cin Hanci A Jihar Kano

Daga Maigari Abdulrahman,

Gwamanan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin tsara dabarun yaki da cin hanci domin yaki da cin hanci a Jihar.

A yayin kaddamar da kwamitin ranar Alhamis a Jihar Kano, gwamnan ya ce, manufar kwamitin ita ce samar kawar da cin hanci da rashawa, tabbatar bin doka da oda, da kuma yin gaskiya a cikin gudanar da ayukka.

Gwamnan, wanda sakataren gwamnati, Alhaji Usman Alhaji ya wakilta, ya bayyana cewar, Najeriya ba za ta taba samun cigaban da ake bukata ba da kalar cin hanci da rashawar da ke akwai.

“Ba bukatar sai mun ce rashawa da cin hanci na illata mu a kasar nan, gaskiyar zance ita ce, ba za mu taba samun ci gaba a irin halin cin hanci da rashawar da ke cikin kasar ba,” a cewar gwamnan.

A zamanin mulkinsa, Jihar Kan ta ciri tuta a fagen yaki da cin hanci kuma ta wuce tsara, in ji Gwamna Ganduje. Samar da hukumar, bada dama ne gareta na yin cin gashin kanta ba tare da tsoma bakin wani, kuma gwamnati za ta yi dukkan abinda ya dace na karfafa hukumar, in ji shi.

A cewar sa, a gwamnatinsa tsaye take tsaf don hukunta duk wanda aka sama da laifi, ba wanda ya fi gaban hukunci matsayar ya aikata, kamar yadda za a gani a kwamishinoni biyu da muka sauke bayan samun su da laifin aikita rashawa, in ji Ganduje.

Ganduje ya yaba da samar da kwamitin, inda y ace shi ne mafi dacewar kwamiti da gwamnatinsa ta kafa a tarihi.

“Ina iya cewa, wannna kwamitin na dai daga cikin manyan kwamiti mafi girma da muka yi. Dalili shi ne cewar, kwamitin na da aii biyu ko bangare biyu.”

“Sashen farko shi ne na kai koken jama’a a kan sabani ko wata damuwa, ba lalle miyagun laifuka ba. sai kuma dayan bangaren na yaki da cin hanci da rashawa. Kowane daban ne da daya.”

Daga karshe, ya yi kira ga kwamitin da su samar da ingantattun hanyoyin da zai ba saukaka wa mutane risker hukumar domin kai koke, tare da samun  natsuwar adalci, kuma wannan koda a kan gwamnati ne ko kuma jami’an gwmanati, ya karkare.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin kuma shugaban hukumar, Mista Muhyi Magaji-Rimingado, y ace kwamitin zai yi aiki wurin samar da ingantattun hanyoyin domin yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

Cin hanci da rashawa dai na dai daga cikin musabbabin tabarbarewar al’amurrra a Najeriya, kuma jami’an gwamnati da ‘yan siyasa na kan gaba a masu aikatawa.

Ko a 2018, idan za a iya tunawa, jaridar “Each day Nigerian” ta wallafa wani bidiyo na gwamna Ganduje, inda ake ganinsa yana karbar kudi, abinda mawallafin ya zarga da cewa cin hanci ne gwamnan ke karba, zargin da gwamnatin jihar Kano ta musanta.

A nasa bangaren ma, shugaban kasa Buhari, da yake amsa tambayar ‘yan jarida kan lamarin, ya bayyana rashin gamsuwa da bidiyon, yana mai zargin zai iya zama kagaggen bidiyo ne kuma shiryayye.

 

What's On Your Mind?