Ganduje Na Adalci Ga Dukkan Jami’ai A Kano –Muhuyi Magaji

0
68

Ganduje Na Adalci Ga Dukkan Jami’ai A Kano –Muhuyi Magaji

Shugaban hukumar karbar korafin Jama’a da yaki da cin hance da rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayana cewa, duk wani jami’i ko wani mai riki da mukamin siyasa ko shugaban wata ma’aikata, ko shugaban wata hukuma da ke jihar Kano da ya ce Gwamna Ganduje baya masa komai, to tabbas karya yake yi, kuma duk wanda ya kara fadar haka ku zu zanbako bayanin cikakke akan abin da aka bashi a lissafe, zan fasa kwai.

Manoma 20,000 Za Su Amfana Bashin Noman Rani Na Masara Da Kungiyar MAGPAMAN Za Ta Samar A Jihar Katsina

Barista Muhuyi Magaji ya bayana hakan ne a lokacin da wata kungiya mai goyan bayan Ganduje ta kai masa ziyara a ofishinsa a makon da ya gabata.

Har ila yau, ya ce, shi a matsayinsa na shugaban wannan hukuma, Gwamnan kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi masa komai ta hanyar gyara shalkwatar hukumar kamar yadda ya ke, domin ko a Abuja ginin mu abin kallo ne, kuma Ganduje baya daukar zugi ko jita-jita aka aiyuka.

Ya ci gaba da cewa, in badan nagartar Ganduje ba da yanzu bana kan kujirar, don haka ina mamakin masu zagin Ganduje don na san ba su san nagartar Ganduje ba. Kuma ni kaina ana tsorona a kawo min kauta domin an sha gwadani bana karba duk da ni ban ce ma’asumi ba ne ni, “a cewar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.

What's On Your Mind?