Gamayyar ‘Yan Kwadago Da Fararen Hula Sun Nemi Gwamnati Ta Shiga Lamarin Sace Daliban Kaduna

0
141

Gamayyar ‘Yan Kwadago Da Fararen Hula Sun Nemi Gwamnati Ta Shiga Lamarin Sace Daliban Kaduna

Daga Rabiu Ali Indabawa

Gamayyar kungiyoyin kwadago da kungiyoyin Fararen Hula ta roki gwamnatin tarayya da ta fara aiwatar da abubuwan da ake bukata don gaggauta sakin dalibai da ma’aikatan da aka sace a wata Jami’ar Kaduna.
daliban da wasu ‘yan bindiga suka kai hari jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna a ranar Talata inda suka yi awon gaba da wasu daliban. Uku daga cikin daliban da aka sace daga baya an tsinci gawar su a ranar Juma’a a kauyen Kwanar Bature, a wani wuri kusa da jami’ar.
A martanin da ya mayar, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen “dabbanci” yayin da yake ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe.
Amma a wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Femi Falana, shugaban rikon kwarya na ASCAB, ya ce yin Allah wadai a hukumance bai isa ya magance matsalar tsaro da kasar ke fuskanta ba.
Ya ce ana bukatar matakai na gaggawa don tabbatar da kubutar da daliban da aka sace daga Jami’ar Greenfield, da Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnati, Chibok, jihar Borno, da Kwalejin Kimiyyar Kimiyya ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, Dapchi, jihar Yobe.
“Muna tausaya wa iyaye da dangin daliban da daya daga cikin gungun ‘yan fashi da makami suka yi wa kisan gilla ba tare da fuskantar wani babban kalubale ba a jihohi da dama a shiyyar Arewa maso Yamma,” in ji shi.

“Kamar yadda aka saba, duka gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Kaduna solar yi tir da Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa daliban
“Dole ne gwamnatoci su dauki matakan gaggawa domin kubutar da ragowar daliban jami’ar Greenfield da sauran daliban da aka sace wadanda a halin yanzu suke cikin halin kaka-ni-kayi a hannun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, ciki har da ‘yan matan Chibok da Dapchi.”
A watan Yulin 2020, ASCAB ta zargi gwamnatin tarayya da nuna gazawarta don magance tashin hankali a Arewa. kungiyar ta tuno da samamen wanda ya kai ga ceto wani Ba’amurke da ‘yan bindiga suka sace a Jihar Neja.
Sanarwar ta ce aikin ya samu nasarar ne sakamakon tura jirage marasa matuka da gwamnatin Amurka ta yi, sannan ta kara da cewa ya kamata a tura irin wadannan kayan aikin gano daliban da aka sace da kuma kubutar da su.
“Maimakon kawai shiga halin nuna tausayawa a wasu lokutan ga iyalan wadanda aka sace wadanda galibi ‘yan fashi ne da ‘yan ta’adda ke kashe su, ya kamata gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi daban-daban su mallaki muhimman kayan tsaro don bin diddigin gungun masu aikata miyagun laifuka wadanda ke addabar ‘yan kasar da ba su dauke da makami,” in ji shi. .
“Tun da ya kamata gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna su dauki cikakken alhakin kisan gillar da aka yi wa marassa karfi da sauran ‘yan kasa da wasu masu laifi ke yi jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba.

What's On Your Mind?