Matasan Arewa: Gaba Kura Baya Siyaki

0
79

Gaba Kura Baya Siyaki

Kowace kasar duniya na alfahari da matasan cikinta domin kuwa su ne dukiyarta. Da su ne take takama, ta ke kuma alfahari, domin ta kan su ne ake bi a tabbatar da dorewar al’amura da harkokin ciyar da kasa gaba ko kyautata halayen zamantakewar al’umma. kasar duk da ta dace da samun ingantattun matasa, managarta, to ita kam sai a yi mata barka domin kuwa cikin ruwan sanyi aikace-aikacen shugabanninta za su yi ta kankama, za su kuma samu mataimaka tsayayyu, wadanda za su magance dukkan matsalolin da za su kunno kai har su hargitsa lissafi da kuma dagewa wajen habaka kyawawan manufofin hukumomi don kirkiro arzikin da zai wadaci kowa da kowa. Amma idan aka yi rashin sa’a wata kasa ta zamanto ba ta da matasan da za su iya jajircewa don tagazawa magabatansu, sa’annan kuma ba su iya tabukawa don taimakon kansu, to tabbaci hakika wannan kasa ta kama hanyar daidaicewa domin kuwa dukkan al’amuran shugabanninta za su  karkace, harkokinta za su tsaya cik, sa’annan kuma tattalin arzikinta zai tabarbare.

A takaice dai ana iya cewa matasa su ne jigon tallabar al’ummar da ya kamata a kula da su yadda ya kamata da kuma nuna masu dabarun karfafawa da kuma wasa kaifin hankalinsu; a kuma yi masu tanadin dukkan abubuwan da za su bukata don kyautata rayuwarsu; a kuma dora su bisa turbar da za su kai ga inda za su koyi tsananin kishin kasarsu har su gano hanyoyin kare martabarta da kuma daga matsayinta a duniya. To amma su wane ne za a  kira matasa? Matasa dai su ne mutanen da shekarunsu suka kama daga goma sha biyar zuwa arba’in a duniya. A yanzu haka idan aka gwada yawan matasan da ake da su za a taras photo voltaic kusa kai sulusainin yawan jama’ar kasar nan. Ashe ke nan matasa suna da muhimmanci  a dukkan fannonin rayuwa, suna iya kawo cigaban kasar cikin hanzari, suna kuma iya taka mata birki, komai ya tsaya cik.

Gaba Kura Baya Siyaki

Wannan babban dalili ne da zai wajibtawa gwamnatoci mayar da hankulansu ga harkokin da suka jibanci matasa, domin kuwa su ne manyan gobe, wadanda za su dora daga inda mazan jiya suka gaza, kuma idan su ma photo voltaic suke tun farkon tashinsu to za a yi haihuwar guzuma ke nan, diya kwance, uwa kwance. Shi ya sa  su ma iyaye ke ta yin fafitika don tabbatar da cewa photo voltaic kyautata rayuwar ‘ya’yan da za su gaje su, ba domin gwiwowinsu ne za su dafa, su mike ba a ranar tashin kiyama ba kadai, su ne za su zamanto bangon da iyayen za su jingina da su yayin da karfinsu ya kare a nan gidan duniya. Shi ya sa a wannan marrar da ake ciki ta kasance mawuyaciya sakamakon  mawuyacin halin rayuwa da kuma tsananin rashin aikin yin da ya zama ruwan dare, gidan kowa akwai alamunsa. Al’amarin ya tsananta har ta kai da da da uba photo voltaic zame tamkar matan aure, duk zaman kulle suke yi a gida, saboda rashin aiki yi ya hana su fita zuwa ko’ina.

Wannan babban abin takaici ne, musamman ma ga iyayen da suka yi ta fafitikar tura ‘ya’yansu makaranta, har zuwa manyan jami’o’i don su samu ilmin da zai ba su damar samun aiki mai tsoka ta yadda za su ji dadin taimaka musu yayin da suka yi ritaya, suna kwanciya a gida don hutawa. To amma hutun ba zai gan su ba, domin kuwa a lokacin ne za su fara wani sabon hakilon ciyar da iyali, ciki har da wancan dan da suka tura jami’a don ya samo digirin-digirgir, domin ba shi da yadda zai yi, shi kuma ba zai shiga uwa duniya ba a yi asararsa, ko ya biyewa masu budurwar zuciya, yana jawo wa iyayensa magana.

Mabiyan Gwamnan Bauchi Sun Sauya Sheka Zuwa APC Bisa Watsar Da Su

To, ko ga su ‘ya’yan ma wannan babbar matsala ce, domin kuwa rashin aikin yi zai iya karya masu zuciya, ganin cewa ‘ya’yan wane da wane photo voltaic kammala karatun jami’a fiye da shekaru shida ba su da aikin yi sai tsofaffinsu ne ke cishe su, saboda haka nan za su fara tunanin dawowa daga rakiyar karatu mai zurfi. Amma idan suka kwantar da hankulansu, suka sake wani karatun ta-natsu a tsanake, sai su fahimci cewa ai hakan ba abin damuwa ne ba, domin gara a ce matashi nada ilmi, ba shi da aiki, maimakon a ce ba shi da aiki kuma ba shi da ilmin. To da wanne zai ji? Wuya dai mawuciya ce, kuma al’amarin duniya ba tabbatacce ne ba, watan-wata rana sai a yi juyin-juya hali, manemin aikin ya zamanto mai daukar aikin. To fatarmu anan shi ne Allah Ya tabbatar da haka ga dubun-dubatan matasan da suka dade da sauke karatun jami’a, har watakila wasunsu photo voltaic fara fitar da zuciya recreation da samun aikin Bature. Allah kuma ya sa hakan ya tabbata, iyayen da suka yi dawainiya da su  da ransu, ba su kwanta dama ba, su samu dan agaji daga ‘ya’yansu, ko da kuwa na sayen gishirin miya ne ko na itacen wutar da za a hura don jin dimi a zaure.

To yayin da rashin aikin yi ke ragewa matasa gardin rayuwa akwai kuma matsalolin da ke kuntatawa matsa, wadanda ba za a iya cewa suna da hannu wajen afkuwarsu ba, ko suna iya turzawa wajen kawar da su. Wadannan kuwa su ne wasu al’adun da al’ummomin Arewa suka jajibo da rana tsaka, suka sanya su cikin harkokin zamantakewa. Da farko dai gurbacewar kyawawan dabi’unmu na auratayya cikin sauki da mutuntaka, photo voltaic kau, an tsiri irin na Yahudu da Nasara wadanda ba a batun mutunci ko zumunci wajen wanzar da su sai dai kudi kawai. Idan kuma kana da su kai ne za ka yi aure na garari, idan kuma ba ka da su kana ji, kana gani auren zai gagare ka, kuma idan ba ka angwance ba sa’ilin da kake dan bana-bakwai ta ina za ka samu kwanciyar hankali bayan ka kai minzalin mutumin da ya kamata ya zama magidanci? Ba shakka batun wahalar aure ga matasa na daga cikin al’amuran da ke jefa matasan kasar nan cikin mawuyatan lokutan da za su ba su daman koyon miyagun dabi’un da za su nakasa rayuwarsu.

A ‘yan shekarun da suka gabata iyaye ne ke yi wa yaro aure da zaran an yi masa bante, domin kuwa ba a bukatar abin duniyar da ya wuce sadaki da kayan lefe kafin a yi biki. Kuma a lokacin cikin sauki iyayen yaro ke gina masa turakar da amaryarsa za ta tare, a kuma yi shagalin da zai kayatar da kowa ba tare da sai ‘yan uwa da iyaye photo voltaic shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi  ba kafin bayar da gudummawarsu  domin fita kunyar bikin dangi.

Wannan al’amari ya shafi dukkan matasa ne, maza da mata, domin kuwa ko da yarinya tana makarantar boko, ko kuma ta kammala, sai ta rika kamar kubewar fadama a gidan iyayenta kafin a samu wanda zai taya ta, ba domin ta rasa masoya ne ba a’a mai son ne ba shi da halin sauke dimbin nauyin da iyayenta suka dora masa kafin a rufa ta, a kai ta gidansa. Wasu kuma iyayen ne ba su da halin sayen gado [an Dubai, da kabod din Alaba Market da talbijin Bango da firij da kuma firiza da darduma ko labulen daki na gagari. Idan ma har  wadannan photo voltaic samu, to  za a fuskanci matsaloli recreation da bukukuwan cin abincin dare da na rana, tare da abokan ango da kawayen amarya a wuraren alfarma, sa’annan kuma za a yi wasu tsatsibe-tsatsiben da ba su da tushe a al’adance ko wata makama a addinance wadanda ake kira ranakun uwa da uba da kuma wani abu wai shi Kauye Day.

What's On Your Mind?