Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyayi rajista, za su fallasa ‘Yan bindiga

0
39

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Affiliation of Nigeria (MACBAN), na reshnen Ekiti, Adamu Abache, ya goyi bayan ayi wa makiyaya rajista.

Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyayi rajista, za su fallasa 'Yan bindiga

Alhaji Adamu Abache ya yi kira ga gwamnatin jihar Ekiti, ta yi wa duk makiyayan da ke zama a Ekiti rajista domin aji dadin gane duk wani mai kiwon dabbobi.

Jaridar Vanguard ta ce Adamu Abache ya bukaci ayi wannan rajista ne a kananan hukumomin da makiyaya su ke zaune, su na kiwo ba tare da sun saba doka ba.

Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyayi rajista, za su fallasa 'Yan bindiga

“Makiyaya da ke zaune a Ekiti su na neman zaman lafiya, kuma za mu cigaba da zama lafiya da wadanda su ka tarbe mu. Za mu cigaba da ba gwamnati goyon baya.”

Yan Boko Haram sun kafa sababbin sansanoni, sun boye a Adamawa da Yobe

Ya ce: “Gwamnati ta taimaka mana ta hanyar ba ‘yan kungiyarmu katin da za a rika gane mu, domin makiyaya su na fuskantar kalubale wajen bayyana kansu a jeji.”

“Dole gwamnati ta san inda mu ke, da inda mu ke harkokinmu, duk wanda ya yi wani laifi, za a iya damke shi, a mika shi a hannun jami’an ‘yan sanda.” inji Abache.

Abache ya yi kira ga mutanensa su tona duk wani makiyayi da ke yawo da makamai, ya na ta’adi. Shugaban kungiyar MACBAN ya ce yin hakan zai tsare mutuncin makiyaya.

Jagoran na Miyetti Allah ya ce idan ana bankado bata-gari da ke cikinsu ne za a gane cewa akwai makiyayan kwarai wadanda kiwo su ke yi, ba yi wa jama’a ta’adi ba.

Alhaji Abache ya yi wannan bayani ne a lokacin da kwamitin ‘yan sanda da hulda da jama’a watau PCRC ya kira wani zama tsakanin duka kabilu a garin Ado Ekiti.

A jiya ne Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi ya fito ya na cewa dole ce tasa makiyaya su ka dauki bindigogi, ya ce makiyaya basu da wata mafita illa su yi hakan.

Kamar yadda ya gwamnan na Bauchi ya fada, laifin duk aika-aikar da makiyayan su ke yi, ya rataya ne a wuyan gwamnati da al’umma da su ka gaza basu kariya.

Bala Mohammed ya caccaki gwamna Samuel Ortom a jawabinsa, maganar dai ta jawo ce-ce-ku-ce.

What's On Your Mind?