FRSC Za Ta Fara Aiwatar Da Dokar Sanya Hular Kwano Ga ‘Yan Achaba A Nijeriya

0
191

FRSC Za Ta Fara Aiwatar Da Dokar Sanya Hular Kwano Ga ‘Yan Achaba A Nijeriya

Hukumar FRSC ta bayyana cewa, a halin yanzu ta umarci dukkan jami’anta a sassan kasarnan da su ja dammara tare da tabbatar da aiki da dokar sanya hular kwano ga dukkan masu amfani da mashina musamman ‘yan achaba a kasarnan, jami’in watsa labarai na hukumar, Mr Bisi Kazeem ya sanar da haka a tattauanawarsa da manema labarai ranar Litinin a garin Abuja.

Ya kuma ce, aiwatar da dokar ya zama dole saboda irin asarar rayukan da ake yi in har an samu aukuwar hatsari da mashin.

Ya ce, sa hular kwano na rage matsalar da akan samu in har an yi hatsari musamman irin kariyar da ake ba bangaren jiki masu mahimmanci kamar su ido da hanci da kuma kwakwalwa, yana kuma ceto rayuwar al’umma gaba daya.

Dole ne a kalli Bidiyo Yadda Cikin Alhini Sadiya Kabala ta bayyana yadda sunka Rabu Da Jamilu Shinkafi Kafin yayi Hatsari Ya Rasu

“Sanya hular kwano yana sanya natsuwa ga mai tuka mashin yana kuma kare rayuwa gaba daya, bayanin ya kuma nuna cewa, masu amfani da hular kwano kan kasance cikin wadanda suke tsira in an samu hatsari a kan hanyoyinmu.

Daga nan ya kuma ce, dokar hana mashina hawa manyan tituna a kasarnan yana nan daram, kuma jami’an hukumar za su hukunta duk wanda aka kama yana karya dokar.

What's On Your Mind?