Federal Government ta Bada Umurnin Sake Tantance Masu N-Power

0
157

Gwamnatin Tarayya ta umurci masu amfana da shirin aikin matasa na N-Power da ba su samu allawusi dinsu ba su tafi a tantance su

Gwamnatin ta ce tantancewar ya zama dole ne domin an gano akwai wasu da ke karbar albashi a maaikatun gwamnati kuma su karbi na N-Power

An umurci wadanda za su tafi tantancewar su tafi da wasu muhimman takardu kuma za a kammala a ranar 13 ga watan Oktoba

Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda ThePunch ta ruwaito.

Ta ce an bada umurnin ne domin warware wasu matsaloli da ke suka janyo jinkiri wurin biyan wasu daga cikin masu N-Power din.

FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power

A cewarta, binciken da ofishin Akanta Janar na kasa ta yi bayan wasu solar koka cewa ba su samu allawus dinsu ba ya nuna akwai wasu da ke karbar albashi daga maaikatun gwamnatin tarayya kuma suka karbar allawus na N-Power.

Ministan ta ce wannan tantancewar za ta bawa wadanda abin ya shafa dama su tantance sahihancinsu domin a cigaba da biyansu allawus dinsu da suka yi saura.

Boko Haram: Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sauran sabbin makamai na zamani

“Ana umurtar masu amfana da shirin N-Power su tafi ofisoshin jihohinsu tare da lamban asusun bankunansu, har da takardar hada hadar bankinsu tun daga watan Maris zuwa yanzu, takardar shaidar kammala NYSC, takardan shaidan haihuwa da sauran takardu don a tantance su,” inji Faruk.

Ta ce a ranar 13 ga watan Oktoban 22 za a dakatar da aikin tantancewar.

Ministan ta kuma ce dukkan wadanda ba su hallarci tantancewar ba ba za su samu allawus dinsu ba.

A wani labarin daban,Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Aliu, masana’antar masu nishadantarwa da gwamnatin jihar Ekiti bisa rashin fitaccen mai wasan drama, Jimoh Aliu. Jimoh Aliu ya rasu yana da shekaru 80a duniya kamar yadda The Pulse ta ruwaito.

What's On Your Mind?