Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023

0
25

Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023

Fastocin kamfen din gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya billo a wasu manyan hanyoyi a jihar Kano, jaridar Every day Belief ta ruwaito.

An gano fastocin da ke dauke da rubutun da ke nuna kudirin gwamnan na neman shugabancin kasa a 2023, a wasu yankunan cibiyar kasuwancin na arewa.

A cewar rahoton, fastocin basa dauke da logon kowacce jam’iyya amma akwai babban rubutu da ke cewa “Don samun chanji 2023, ku zabi Yahaya Bello a matsayin Shugaban kasar, Jumhuriyar Najeriya.”

An manna fastocin a wasu muhimman wurare a jihar, ciki harda Murtaa Muhammad Means, hanyar filin jirgin sama da kuma hanyar Sani Marshal.

Sauran yankunan da aka gano fastocin sun hada da hanyar Race Course, hanyar Bompai da wasu yankuna na unguwanni gidan gwamnatin Kano.

Wasu yan Najeriya a shafin Twitter sun yi sharhi a kan fastocin.

Akibu Oluwaleke Waliu ya rubuta:

“Ko kamshin tikitin hawa kujerar Shugaban kasar Najeriya ba za ka ji ba a 2023.”

Ma’aji Umar ya rubuta:

“Wannan mutumin na so ya wofantar da kudin Kogi, wani ya fada masa idan lokaci ya kure.”

Ralph Eboigie ya rubuta:

“Ko zaben fidda gwani ba zai ci ba. Gwamnan da ya kasa. Babu wani abun rubutawa recreation da shugabancinsa a Kogi.”

A wani labarin kuma, hadimin tsohon gwamnan jihar Imo, Sam Onwuemeodo, ya bayyana abin da ya hana mai gidansa Rochas Okorocha, zuwa wani taro na APC da aka yi.

Kwanan nan wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na yankin Kudu maso gabashin Najeriya sun hadu sun yi wani taro a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Owerri.

Sam Onwuemeodo ya yi bayanin abin da ya sa Rochas Okorocha bai samu halartar wannan taro ba.

What's On Your Mind?