Farin Jinin Arsenal Ya Fara Dusashewa

- Advertisement -

Farin Jinin Arsenal Ya Fara Dusashewa

Daga Abba Ibrahim Wada

Da alama farin jinin da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke wasa a gasar Firimiya ta Ingila take dashi na ci gaba da dakushewa sakamakon rashin nasarorin da take samu da kuma kasa katabus a gasar wasanni hudu da ta shiga bana amma ta kasa kai labari ko a guda daya.

Shan kashin da kungiyar tayi daga gasar cin kofin Europa a hannun kungiyar kwallon kafa ta billareal wadda ta fitar da ita daga gasar cin kofin Europa bayan karawar da suka yi sau biyu ya kawo karshen duk wata fata na lashe kofi da kungiyar ke da ita a kakar wasa ta bana.
Bayan nasarar da billareal ta samu akan Arsenal a makon jiya da ci 2-1,kungiyar da tsohon manajan Arsenal Unai Emery ke koyarwa ta bita har London inda suka tashi ba tare da wata kungiya ta samu nasara ba, abinda ya sa ta fitar da Arsenal daga gasar baki daya.

Dama kuma wannan shine kofi daya tilo da ake saran Arsenal zata taka rawar ganin saboda yadda aka cire ta a gasar kofin kalubale na FA da kofin Carabao Cup, ya yin da take matsayi na 9 a teburin Firimiyar Ingila.

Wadannan rashin nasarori ya sa kungiyar ta koma na ‘yan baya ga dangi wajen rasa kimar ta da kuma hana ta samun damar karawa a nahiyar Turai a kaka mai zuwa saboda gazawar ta na zama cikin kungiyoyi 6 na farko a teburin Firimiya.
Publicité
Kociyan kungiyar,  Mikel Arteta ya ce solar yi iya bakin kokarin su wajen ganin solar samu nasara amma kokarin na su bai isa ba, kuma kowanne daga cikin su na da alhakin yanayin da kungiyar ta samu kan ta a halin yanzu.

Tuni wasu tsofaffin ‘yan wasan kungiyar suka fara bayyana ra’ayoyin su wajen ganin anyi gyara kan yadda ake tafiyar da ita wajen kashe kudi domin saya mata ‘yan wasan da suka dace da zasu dawo da kimar ta a gasar Firimiya da kuma Turai.

Nan Gaba Zan Samu Nasara A Arsenal – Arteta
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana cewa duk da halin da kungiyar take ciki a yanzu, amma yana da yakinin cewa zai samu nasara a kungiyar idan har suka ci gaba da bashi lokaci.
Arteta ya bayyana haka ne bayan Arsenal ta yi ban kwana da gasar Europa League ta bana, bayan da ta tashi Zero-Zero da billareal a Emirates ranar Alhamis saboda a wasan farko da suka fafata a makon jiya a Spaniya a wasan daf da karshe, billareal ce ta yi nasara da ci 2-1, kungiyar Spaniya ta kai zagayen gaba da kwallo 2-1 kenan gida da waje.
Arsenal wadda ta sa ran kai wa wasan karshe domin lashe Europa League na bana ta shiga tsaka mai wuya ganin tana mataki na tara a kan teburin gasar firimiya ya yinda ya rage wasanni hudu a karkare kakar wasan bana.
Arsenal wadda ta yi shekara 20 tana zuwa Champions League a jere ta koma buga Europa League, wanda sai ta yi da gaske sannan zata  samu shiga gasar badi ta kakar wasa ta 2021 zuwa 2022.
“Tabbas bamu samu abinda muke fatan samu ba a wannan kakar amma duk da haka ba a kammala kakar wasa ba kuma ina da yakinin cewa nan gaba zan samu nasara a kungiyar Arsenal” in ji Arteta
Arsenal ta kai karawar karshe a Europa League a shekarar 2019 karkashin kocin billareal, Unai Emery, amma ta yi rashin nasara da ci Four-1 a hannun Chelsea kuma wannan karon  tsohon kocin Arsenal, Unai Emery ne ya yi waje da Arsenal a Europa League na bana.
Cikin watan Nuwambar shekara ta 2019 aka sallami mai koyarwa Uni Emery daga jan ragamar kungiyar ta Arsenal, bayan watanni 18 yana jan ragamar kungiyar, inda Mikel Arteta ya maye gurbinsa.
Wasannin Premier League da suke gaban Arsenal:
Premier League Lahadi 9 ga watan Mayu
Arsenal da West Brom
Premier League Laraba 12 ga watan Mayu
Chelsea da Arsenal
Premier League Laraba 19 ga watan Mayu
Crystal Palace da Arsenal
Premier League Lahadi 23 ga watan Mayu
Arsenal da Brighton

- Advertisement -