Farfesa U G Dambatta Ya Yaba Wa Adnan Kan Rubuta Littafin Dambazau

0
76

Farfesa U G Dambatta Ya Yaba Wa Adnan Kan Rubuta Littafin Dambazau

Daga Mustapha Ibrahim Kano

Shugaban hukumar NCC Farfesa Umar Garba dambatta wanda ya zama daya daga cikin dinbum manyan baki da suka halarci kaddamar da littafin Malam Yunusa Dabon Dambazau wanda Malam Adnan Bawa Bello ya rubuta, Farfesa UG dambatta ya yaba wa wannan marubuci kan wannan kokari da yayi wajen bayyana tarihin da ya shafi wannan bawan Allah Dabon Dambazau da ma sauran abubuwan da suka shafi tarihi na Dambazawa baki daya, dan haka wannan abun a yaba ne kuma ayi koyi da aikin wannan marubuci da kuma abubuwan da ya fada na alkhairi a cikin wannan littafi mai dimbin tarihi ga Dambazawa da ma al’ummar Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya.

Farfesa UG dambatta ya bayyana haka ne a lokacin taron kaddamar da littafin da akayi a daki taro na makarantar nazarin shari’a ta Malam Aminu Kano wato LEGAL a ranar a karshen mako da ya gabata.

Har ila yau ya bayyana cewa Makoda da dambatta abu daya ne dan haka yana ganin cewa mutanen dambatta da Makoda da ma sauran al’ummar Jihar Kano solar cancanci yabo akan kokarin su na bunkasa ilimi da tattalin arziki da ma abun da ya shafi zaman lafiya a Kano da Najeriya baki daya.

Shi ma marubucin wannan littafi Malam Adnan Bawa ya bayyana farin cikin sa kan yadda mutanen dambatta da Makoda da sauran al’ummar Kano da jami’an gwamnati suka taka muhimmiyar rawa wajen kaddamar da wannan littafi da ya rubuta ya ce ya kuma iya kokarin sa na binciko tarihin wannan bawan Allah wanda ya bada gudunmawa mai yawa a bangaren cigaban addini, sarauta da sauran al’amura da suka karawa Dambazawa tarihi da kuma daukaka tun a wancan lokaci har zuwa yau. Wakilin mu dai ya rawaito mana cewa mutane da dama ne suka halarci wannan taro da aka yi, kadan daga ciki akwai Malam Abba Dabo tsohon dan jarida, Arc. Aminu Abubakar Dabo da Sheikh Ibrahim Khalil da sauran masu rike da mukaman siyasa da sauran masu rike da mukamin sarautar gargajiya, yan kasuwa da sauran al’umma wanda marubuci ya yabawa kan wannan gudunmawa.

What's On Your Mind?