Farfesa Hafsat Na Bayar Da Gudumawa Ga Matan Kano – Balaraba Ibrahim Ahmad

- Advertisement -

Farfesa Hafsat Na Bayar Da Gudumawa Ga Matan Kano – Balaraba Ibrahim Ahmad

Daga Ibrahim Muhammad,

Mai baiwa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin ma’adinai, Hajiya Balaraba Ibrahim Ahmad ta bayyana matukar jin dadinta bisa irin gudunmawar da mai dakin Gwamnan Kano Ferfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ke bayarwa ga cigaban Mata musamman wajen basu manyan mukamai a Gwamnati.

 

Ta bayyana hakanne da take hira da ‘yan jarida a Kano, inda ta ke cesa, Hajiya Balaraba ita a matsayinta ta ‘yar siyasa wacce ta dade a tafiyar siyasa ba ta ga wata Gwamnati da a ka yi da ta kai wannan kulawa da cigaban Mata ba, yadda mai dakin mai girma Gwamna Farfesa Hafsat da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suke kulawa da bai wa mata manyan mukamai na Gwamnati.

 

Ta ce, a sarari ya ke domin itama kanta misali ce don ita ce mai bai wa Gwamna Ganduje Shawara kan harkokin ma’adanai.

 

Ta kara da cewa, ire-irenta masu manyan mukamai a wannan Gwamnati suna da yawa, tun daga kan kwamishinoni mata da masu bai wa Gwamna shawara da manyan mataimaka ga Gwamna na musamman.

 

Ta ce, Gwamnatin Ganduje ta yiwa mata tagomashin da ya taba zuciyar su ya kuma kara musu so da kauna da kara biyayya ga manufofin Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da kuma goyon baya ga duk abinda take so. Domin tun da ake siyasa a Kano ba a taba bai wa mata damar zama kansila mai gafaka ba, sai a wannan Gwamnati da matar Gwamna ta ce kowace shugabar mata ta jam’iyya a kananan hukumomi 44 a basu matsayin kansila mai gafaka, kuma ta yi kota kawo wanda zai yi a madadinsa.

 

Balaraba Ibrahim ta kafa misali da kanta a matsayinta na mai bai wa Gwamna shawara kuma daya daga cikin masu ruwa da tsaki a siyasar karamar Hukumarta ta rabauta da wannan dama ta kai wacce ta cancanta aka yi ma ta kansila don haka ba abinda za suce da wannan Gwamnati ta Ganduje sai godiya.

 

Ta ci gaba da cewa, Gwamnati ce da take tafiya da mata, da kuma rabon tallafi jari da Matar Gwamna Farfesa ta ke akai-akai a kananan hukumomi yanzu haka ana bi daya bayan daya ana bai wa mata tallafi na jari don dogara da kai su rike iyalansu su rikan taimakon mazajensu ba sai solar raja’a akan kullum sai miji ya basu ba.

 

Hajiya Balaraba Ibrahim Ahmad ta ce, alkhairin matar mai girma Gwamna Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje mai girma ne, zata yi makashi tsakaninka da ita, ta baka da hannun dama na hagu ma bai sani ba.

 

Ta ce, a wannan Gwamnati akwai manyan sakatarori mata , hatta shugabar ma’aikata ta Kano mace ce. Bangarori da yawa na mukaman siyasa mata da yawa a bangarori da yawa.haka suke so sauran Jahohi na kasarnan suyi koyi da Kano wajen kulawa da cigaban mata da ake samun nasara ake aiwatarwa bisa c irin shawarwari da mai dakin Gwamna Farfesa Hafsat take bai wa mijinta, saboda ita mace ce tasan ciwon ‘ya mace, yawan akwai aikin da in ka bai wa namiji bai son yadda zai tafi dashi ba saboda aikin na Matane dole ne sai an samu ana bai wa mata ana tafiya dasu saboda a rinka daidaito.

 

Ta kara da cewa, abinda ya shafi mace asa mace ta jajirce akai, ita ta son ciwon mace, abinda ya shafi namiji shima ya jajirce domin shi namiji a kowane bangaren yana da rawar da yake takawa mai muhimmanci cikin rayuwar mata don haka a jajirce a bai wa mata hurumin da zasu kawo ‘yan uwansu mata cigaba.

 

Ta yi kira da a cigaba da wayar da kan mata wajen shiga harkokin siyasa, domin da yawa basu da wayewar shiga siyasa, saboda suna gani kamar harka ce ta rashin kamun Kai, ko mata wadanda suke ciki ana ganinsu kamar marasa da ido saboda yadda ake cudanya da maza a wasu lokutan, alhali kuwa ba haka ba ne ita mace duk inda ta sami kanta ya danganta da yadda take mu’amalarta yadda ta tsare kanta haka za a dauketa ko tana da aure ko bata da miji, kullum ana tsammaninta ta zama mai kamun Kai da daraja a ko ina take.

 

Don haka yakamata mata da suke gefe suke kallon ‘yan siyasa daga waje su shigo a yi tafiya dasu, musamman wadanda suke da ilimi ko daliban ilimi, saboda yawanci wasu suna ganin su dalibai ne suna nuna ba ruwansu da siyasa, amma ko a makaranta akwai nazarin siyasa da ake, saboda haka ko mai mutum yake a rayuwar siyasa zata iya zama daga cikin harkokinsa na rayuwa ta yadda zaka iya zuwa ka kawo sauyin a harkokin rayuwa in kana ganin akwai wani abu na gyara kai da ka ke gefe ka hango, kamar yadda Bahaushe ke cewa mai kallon tamaula yafi mai bugawa iyawa, saboda yana gefe yana cewa idan mai buga kwallon yayi haka ya buga da ta shiga raga.

 

Amma shima idan ya shigo gyaran da yake gani a waje sai ya yi a sami nasara, wannan zai kawo cigaba a kuma tsaftace harkar siyasar.

 

Ta ce, tana kira ga Mata da azo a hadu a hada karfi da karfe a taimaki juna a kawo cigaba a samu maganta barazanar tsaro wanda yayi katutu saboda rashin hadin kai, saboda kai ka nade hannunka kana ganin cewa Gwamnati ce takeda hakkinda zata kareka ko kuma ta hana wani abu ya faru dakai ba daidai bane.

 

Kowa yana da hakki, harkar tsaro dole sai an hada kai gaba daya an taimaki juna domin Gwamnati kadai bazata iyaba. Sarakuna baza su iya ba duk wani mai mukami ba zai iya ba, hukumomin tsaro baza su iya ba su kadai dole sai an hadu an tainaka wa juna.

 

Hajiya Balaraba Ibrahim Ahmad tace ko a baya ma Gwamna Ganduje yayi aiki da mata a baya kuma sunyi aiki tukuru dan yanada kyau a rika ba mata dama kar a rika ganinsu a ba zasu iya ba, duk da cewa su masu raunine, amma zasu iya bada gudummuwa muhimmiya domin idan ka bai wa mace daya ilimi ka baiwa al’umma ne, idan kuwa namiji ne shi kadai ka baiwa, bazai shiga al’umma ba.Amma duk abinda zaka yiwa mace daya daga hannunta zai je wajen mutum 1,000 daga nan zasu sake zaga dubbai.

 

Don haka ta ce, wannan Gwamnati ta Gwamna Ganduje da iyalansa suna kokari sosai wajen dan bunkasa cigaban mata a jihar Kano.

- Advertisement -