Faransa Ta Gayyaci Benzema Domin Buga Mata Wasa

- Advertisement -

Faransa Ta Gayyaci Benzema Domin Buga Mata Wasa

Daga Abba Ibrahim Wada

Mai horar da kungiyar kwallon kafar kasar Faransa, Didier Deschamps ya gayyaci tauraron dan wasan Actual Madrid Karim Benzama cikin tawagar kasar da za su buga wasa a wasannin gasar cin kofin Turai da za su gudana cikin watan gobe.

Wannan ya kawo karshen dakatar da sanya Benzema cikin tawagar kasar tun daga shekarar 2015, inda yanzu ya shiga cikin jerin ‘yan wasan da za su takawa Faransa wasa a gasar da za’a fara ranar 11 ga watan gobe zuwa 11 ga watan Yuni.

Mai koyarwa Dechamps ya ce akwai matakai daban daban da aka bi kafin gayyatar Benzema, kuma ya gana da dan wasan inda suka tattauna akan kiran nasa da kuma matakan da aka dauka kafin daukar matakin.

Benzema da ya jefawa Faransa kwallaye 27 a wasanni 81 da ya doka mata na daga cikin ‘yan wasa irin su Kylian Mbappe da Antoine Griezmann da za su sanya rigar kasar su a wasannin na Euro.
A wannan kakar mai karewa, Benzema ya jefawa kungiyarsa ta Actual Madrid kwallaye 29, abinda ya zarce kwallaye 20 da ya saba jefawa kowacce shekara tun bayan da Cristiano Ronaldo ya bar Actual Madrid zuwa Jubentus a shekarar 2018.

Sauran ‘yan wasan da suka shiga tawagar Faransa solar hada da dan Barcelona Ousmane Dembele da Olibier Giroud da Marcus Thuram Kingsley Coman da Paul Pogba da kuma Thomas Lemar sannan masu tsaron raga solar hada da Hugo Lloris da Mike Maignan da kuma Stebe Mandanda.

Benzema  ya yi shekara biyar da rabi rabon da ya buga wa kasarsa wasa, bayan wani faifan bidiyo na lalata da ake zarginsa da kokarin cin dunduniyar wani dan wasan tawagar, Matheu Balbuena
dan wasan mai shekara 33 a duniya zai fara yi wa kasar wasa a karon farko tun bayan watan Oktoban shekara ta 2015, inda ake sa ran zai buga gurbin masu cin kwallo tare da Kylian Mbappe da kuma Antoine Griezmann,
Har ila yau Karim Benzema ya zama gwarzon dan kwallon kasar da ya yi fice a bana a ‘yan wasan da ke buga wasa a waje da kungiyar kwararrun ‘yan wasan Faransa suka zaba ranar Talata.

dan wasan wanda ya ci wa Actual Madrid kwallo 29 a bana, ya yi bajintar zura kwallo fiye da 20 a kaka uku kenan tun bayan da Cristiano Ronaldo ya bar Santiago Bernabeu ya koma Jubentus a shekarar 2018.

Faransa za ta fara gasar cin kofin nahiayr Turai da Jamus a birnin Munich ranar 15 ga watan Yuni, kwana hudu tsakani ta fafata da kasar Hungary a birnin Budapest sannan za kuma ta karkare karawa ta uku ta cikin rukuni na shida da Portugal ranar 23 ga watan Yuni.
kungiyar kwararrun ‘yan kwallon Faransa ce ta bayyana Benzema a matakin wanda ba kamarsa a kakar kwallon kafa  ta 2020/21 da ke buga wasa a waje kuma cikin wadanda ya yi takara da su solar hada da Hugo Lloris, mai tsaron ragar Tottenham da N’Golo Kante na Chelsea da Paul Pogba na Manchester United da Ousmane Dembele na Barcelona da Ferland Mendy na Actual Madrid da sauran su.

Wannan ne karo na biyu da Benzema ya lashe kyautar bayan shekara ta 2019, duk da cewar Didier Deschamps baya gayyatarsa tawagar kwallon kafar Faransa amma Benzema ya ci wa Actual Madrid kwallo 29 a kakar nan, kungiyar da take sa ran lashe La Liga na bana, bayan da take mataki na biyu a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Atletico mai jan ragama.

Wannan kyautar da Benzema ya lashe ta zo ne a daidai lokacin da kociyan tawagar kasar Faransa,  Deschamps ya bayyana ‘yan wasan da za su wakilci Faransa a gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana kuma har da dan wasan.

Tun a bara ya kamata a buga gasar cin kofin nahiyar Turai, amma cutar korona ta kai tsaiko da aka dage fafatawar zuwa shekara ta 2021 kuma a wannan shekarar dai za’a buga wasan guje-guje da tsalle-tsalle na duniya shima wanda aka dage a baya saboda Korona.

- Advertisement -