Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (2): Aiki A Cikin Kwanukan Ne Mafi Soyuwa A Wurin Allah

- Advertisement -

Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (2): Aiki A Cikin Kwanukan Ne Mafi Soyuwa A Wurin Allah

Daga Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani

Yana daga falalar wadannan kwana goma na farkon watan Zulhajji, su ne cikamakon watanni sanannu na aikin Hajji.

Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce Hajji watanni ne sanannu. Tun daga Shawwal watan Hajji ya shiga, yanzu in ka yi umura da azumi ba za ka yi hadaya ba, ba ta hau kanka ba, amma kana shigowa Makka sai aka sanar da ganin watan Sallah (Shawwal), idan ka yi umura to ka yi ta a cikin watan Hajji sai ka yi hadaya. Watannin Hajji su ne Shawwal, Zulkida da Zulhajji, wadannan kwanaki goman na farko su ne cikon lokacin Hajji.

Tun da Arfa an yi ta ranar 9 ga wata, jifa da dawaful ifada an yi su ranar 10, to Hajji ta kare, sauran ayyukan da za a yi nafila ne kawai.

Sannan kwana goman nan na farkon watan Hajji su ne kwanuka sanannu da Allah ya shar’anta yin zikirai a cikinsu, saboda ni’imar kayan dadi da ya ba mu.

Allah bai hore ma wani a duk tsawon shekara ya iya sayen nama ya ci a gidansa ba, amma lokacin layya Allah na iya hore masa ya sayi abin layya ko kuma wani ya yi layyar ya ba shi sadakar nama.

To a bisa wannan ni’ima a yi ta zikiri tun daga farkon wata har zuwa karshen kwanukan sanannu. Zikiran da ake yi a cikin wadannan kwanukan sanannu solar fi falala a kan na wasu kwanukan da ba su ba. kila an ce solar fi falala da kwana dari uku da sittin (kimanin shekara kenan).

kila kuma solar fi da kwana dubu. Ba zikirai ba kawai, duk wani aikin alheri ma a cikin wadannan kwanukan suna da wannan falalar.

Shi ya sa Bayin Allah tun daga kan Sahabbai da Shehunnai idan wadannan kwanukan suka kama, sukan yawaita zikiran da suke yi, har wasu na shiga cikin kasuwanni suna yawo suna zikiri, masu kasuwar ma suna amsa musu, saboda kwanukan na zikiri ne. Naked kuma a ce ranar Arfa da wadannan kwanukan na yanyana nama (Ayyamut Tashrik). Galibi mu nan (a Maz’habar Maliyya ga wadanda ba su je Hajji ba) sai ranar Sallah da Azuhur ake fara zikiran (Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamdu) zuwa Sallar Asubahin rana ta hudu (salloli 15 kenan). Amma a wasu Maz’habobin tun daga ranar Arfa ake fara zikiran.

Bukhari ya fitar da Hadisin da aka karbo daga Ibn Abbas, hadisi ne ingatacce. An karba daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “babu wadansu kwanaki da aiki mai kyau a cikinsu suka fi soyuwa ga Allah daga wadannan kwana goma”. kila Abdullahi Ibn Abbas ya fassara da cewa, Annabi (SAW) yana nufin wadannan kwana goman na farkon Zulhajji. Sai Sahabbai suka tambayi Manzon Allah (SAW) cewa, yanzu ko yaki don daukaka addinin Allah aiki a cikin wadannan kwana goman ya fi shi? Manzon Allah (SAW) ya ce ko shi ne. Sai dai yakin da mutum ya fita da ransa da dukiyarsa kuma ya yi shahada bai dawo ba, wannan ne kadai ya fi aiki a cikin wadannan kwanakin goma. Ma’ana ban da yakin da aka yi nasara aka samu ganima da sauransu. Shi ya sa Malamai suka sha wuya wurin bambance falalar Badar da Ukhudu. Badar an yi nasara, an samu ganima kuma Allah ya yaba da wadanda suka halarta har ya yi musu wata daraja ta daban, amma kuma Ukhudu an sha wuya da sauransu. To in aka dubi wannan Hadisi na falalar yakin da mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo ba, sai a ga Ukhudu ta fi Badar. To amma kuma Badar falala ce da Allah ya ba ta.

Yanzu magana ta zama biyu, akwai maganar falalar wadannan kwanukan da kuma falalar aiki a cikinsu. Wannan Hadisi ya nuna aikin da aka yi a cikin wadannan kwanuka goma ya fi na duk wanda aka yi a cikin wasu da ba su ba a cikin shekara kaf, ba tare da coge kowanne ba. Idan kuwa Allah ya fi son aiki a cikin wadannan kwanukan, to su kansu kwanukan ma solar fi soyuwa a wurin Allah Tabaraka wa Ta’ala. Ya zo a cikin Hadisi da wannan lafazi, “Babu wasu kwanaki da aiki a cikinsu ya fi daga wadannan kwanaki goma”. Wannan Hadisi na biyu mai ruwaya ya ruwaito shi da shakku a cikin lafazin tsakanin “mafi soyuwa ko mafi falala” amma wancan Hadisin na sama ingatacce ne kuma ya ishe mu. Idan aiki a cikin wadannan kwana goma ya fi, kuma ya fi soyuwa a wurin Allah a cikin duk sauran kwanuka; to kenan falalar na kwanukan ne ba na aikin ba, domin aikin ana iya yinsa a wasu kwanukan da ba su ba amma kuma falalarsa ba zai kai na wadannan kwana goman ba. Saboda haka ne Sahabbai suka yi wancan tambayar ta sama da muka kawo.

Kowane irin aiki na alheri a cikin wadannan kwana goman yana da wannan falala. Sai dai kuma, za a iya cewa aikin farilla ya fi duk wata nafila, kenan aikin farillar da aka yi a wasu kwanukan da ba wadannan ba solar fi nafilar da aka yi a cikinsu? Eh, haka ne, to amma kuma su ma a cikin wadannan kwanukan goma akwai aikin farillar, don haka su solar fi farillar da aka yi a wasu kwanukan na daban. Nafilolin da aka yi a cikin kwanukan goma na farkon Zulhajji kuma solar fi wadanda aka yi a wasu kwanukan na daban.

Ya zo a Hadisin Ibn Abbas (RA) (dadi a kan wancan Hadisi da ya fada na sama), cewa, “aiki a cikin wadannan kwanukan goma ana ninka shi (falalarsa) sau dari bakwai”, sai dai madogarar wannan karin (na Hadisi) yana da rauni. Idan Sahabbai suka ruwaito magana ta Annabi (SAW) kowa aka ga ya tsaya a karshen wata magana bai-daya, idan aka samu kari daga wani, in Hadisin ingatacce ne to za a hada shi da karin, sai a ce kari ne na alheri. Amma idan akwai dan dugudugu a cikin madogarar Hadisin, galibi Bukhari ba ya yarda da Hadisin.

Amma sauran masu Hadisi za su iya kawowa, sai kuma su ce ga kari da wane ya kawo, illa dai kuma Ahmdu bin Hambal ya ce wannan raunannan karin ya fi ingataccen kowane malami. Ma’ana ba yarwa za a yi ba, illa dai idan an ga akwai rikici ne da zai sa a yar da Hadisi ingatacce to sai a kyale shi kawai. Da yawa masu karatun yanzu, da solar ji an ce Hadisi raunanna ne sai su ce a yar da shi, a’a, ba haka abin yake ba. Wannan da aka ce raunanna ne ba a lafazin ba ne, daga mazajen Hadisin ne.

Allah ya saka wa Malaman Hadisi da alkhairi da suka fitar mana da wannan. An tambayi Shehu Ibrahim Inyass (RA) shin wai wannan magana ta (tantance karya da gaskiya da Malaman Hadisi suke yi) ba nau’i ce ta gulma ba, Shehu ya ce, a’a, Malaman suna kare wa Annabi (SAW) ne.

Malaman Hadisi suna iya yabon mai ruwaya su ce mai sallah ne, mai ibada ne amma da zarar ya yi santsi kan wani abu a cikin Hadisi sai su ce ba gaskiya ba ne, su raunana shi, saboda kiyaye Hadisan Manzon Allah (SAW).

To wannan ragowar (kari na) Hadisin Ibn Abbas (RA) bai inganta kamar na saman da aka fara kawowa a farko ba.

- Advertisement -