Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (1) 

- Advertisement -

Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (1) 

A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadin alfatihi lima uglik; walkhatimi lima sabak; nasiril hakki bilhakk, walhadi ila siradikal mustakimi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. Wa radiyallahu an as’habi rasulullahi (SAW), wala haula wa la kuwwata illa billahil aliyyil azim. Ya himmatas sheikh ihdri lana bihazal mahdari wal’adifi binazaratin ta’atiy lana bizzafari.

‘Yan’uwa barkan mu da sallah, da fatan Allah ya karba mana ibadunmu na Ramadan da na sauran wadanda za mu yi a wasu watannin amin. Muna godiya ga Allah, Allah a cikin ikonsa da hikimominsa da ba za su kirgu ba yana maimaita mana kwanaki domin ayoyinsa su yi ta bayyana ga masu hankali. Allah yana maimaita mana satuttuka, yana maimaita mana watanni da shekaru. A cikin wadannan Allah ya fifita darajar wasu kwanuka a kan wasu saboda cikar kwanakin, idan kwana bakwai ta cika bisa al’ada; Larabawa sukan cika kirge da daraja (girmama) rana ta karshe a mako, shi ya sa muke idin murnar idi ranar Juma’a saboda mun cika kwana bakwai muna gabatar da ibada, da ganin ayoyin Allah a cikin kwanukan. Wannan baya ga abin da Juma’a ta kunsa na tarihin Annabi Adamu (AS) wanda shi ma abu ne mai girma. Haka nan a cikin watanni 12 da muke da su, Allah ya fifita darajar wasu a kan wasu. A ciki Allah Ta’ala ya kwashi wasu hudu daga ciki ya fifita su suka zama muharramai. Ba wai mu zalunci wani a cikinsu ba, a’a; hatta kanmu Allah ya hana mu zalunta naked kuma ka tabo wani. Yana daga cikin mafi girman wadannan watanni hudu Allah ya rufe shekara da su. Na baya ma (Ramadan) kila shi ma wata ne mai alfarma, sannan Almuharram da Allah ya fara shekara da shi yana cikinsu.

Babu kamar watan da Allah ya cika shekara da shi na Zulhajji (da Larabci ana ce ma watan Zul-Hijjah, da Hausa kuma Zulhajji) wanda a cikinsa ya sanya mana Idi babba, idan ka ji an ce abu babba ka san kuwa yana da girma. A cikin watan ake murnar an cika shekara cur ana ibada, ana ma’arifa, ana alkhairi, don haka a gode wa Allah. Sannan a ciki ne aka cika shikashikan Musulunci (Hajji) da ya zama cikar shari’arsa a ranar Arfa “Alyauma akmaltu lakum dinakum….”. La’ila ha illallahu Muhammadur Rasulullahi (SAW), Sallah, Zakka, Azumi da kuma Hajji. Allah ya cika shikashikan Islam a cikinsa. Amma kuma hakan bai hana imani ya ci gaba da sabuntaka ba, domin kashegari a Minna (Makka) kwana biyu da saukar waccan aya ta cikar shari’a, surar Izha ja’a nasrullahi wal fats’h ta sauka. A ciki ga aya nan tana umurtar Manzon Allah (SAW) ya yi tasbihi tare da tahmidi kuma ya nemi gafarar Ubangiji. Sayyida Aisha (RA) ta ce tun da surar nan ta sauka tasbihan Manzon Allah (SAW) a ruku’u da sujada su ne ‘Subhanallahi wa bihamdihi astagfirullah’. A nan ne mashigar darikoki take. Bayan ayar da ta sauka cewa an cika addini, sai kuma ga Izha ja’a nasrullah ta sauka ana umurtar Manzon Allah ya yi tasbihi da tahmidi da istigfari domin a nuna wannan matakin yanzu na imani ne, waccan da aka cika kuwa na shari’a ce. A makamul Ihsan kuma ana shaura awa biyu ko kwana biyu (babu wanda ya ce ko sati biyu) Manzon Allah ya koma ga Allah karshen aya ta sauka, ita ce ayar suratul Bakra: ‘Wattakuu yauman turja’una fihi ilallahi…’ a ciki ga umurnin Tak’wa (jin tsoron Allah) nan, ga na komawa ga Allah da kuma sakayya ba tare da zalunci ba. Farkon abin da ya fara sauka a cikin ayoyin Alkur’ani “Ikra’a (yi karatu)”, karshe kuma hana zalunci (yadda yake a wancan ayar ta Bakara). Karatu da kuma adalci a tsakanin al’umma su ne ginshikan da ke raya ci gabansu. Shi ya sa Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce, “idan na ce a yi karatu ba ina nufin na addini ba kawai, kowane fanni nake nufi (har a samu Musulmin da za su iya zuwa duniyar wata da sauran abubuwa na ci gaban ilimi)”.

A watan Zulhajji aka cika mana shari’a, matakin sabunta imani kuma ya biyo baya sannan a karshen rayuwar Manzon Allah (SAW) aya ta karshe ta yi magana a kan ihsani. Idan an duba, bayan an yi Ramadan; idin da ake yi shi ma na murnar cikar gabatar da daya ne daga cikin shikashikan Musulunci, wato Azumi. Kenan duk abin da aka yi aka samu cikarsa sai a yi masa murna. Wani Bayahude ya taba ce wa Sayyidina Umar (RA), “kuna nan da wata aya wadda da mu ne (Yahudawa) aka saukar mana za mu rika bikin ranar da ta sauka duk shekara idan ta zagayo”. Sayyidina Umar (RA) ya tambaye shi wace aya ce? Ya ce “Alyauma akmaltu lakum diynakum…” sai Sayyidina Umar ya ce masa “to ai kai mun san kowace rana ce (ayar ta sauka), to wane bikin kake so mu yi ban da wanda muke yi? Ayar ta sauka ce a ranar Arfa, shin akwai wani bikin da jama’a suke taruwa kamar ranar Arfa? Ai wannan Arfar ta isa. Haka nan a ranar Juma’a ce (da ake idin mako), to wane biki kuma za a yi?”.

Watan Zulhajji yana da maganganu da yawa a kan falalarsa musamman kwana goman farko. A kan wadannan kwana goma za mu yi karatu in sha Allah daga wannan makon zuwa abin da ya sauwaka. Idan ya so daga bisani sai mu dora daga inda muka tsaya a kan mu’ujizozin Annabawa da Allah ya ba Manzon Allah (SAW) kuma ya kara masa fiye da nasu, in sha Allah.

Yana daga girman kwana goman farko na watan Zulhajji, Allah Tabaraka wa Ta’ala ya rantse da su a cikin Suratul Fajr “wa layalin ashr”. Rantsuwar ta recreation dare da yinin ranakun a dunkule. Sannan Allah Ta’ala ya rantse da Alfijir din ranar farko na watan “Walfajr”. Allah ya yi rantsuwa da sanannen Alfijir na ranar. Wasu Malamai solar ce wannan Alfijir na ranar farkon watan ne, wasu kuma suka ce ana nufin Alfijir na ranar Sallah (ta Layya) ake nufi, wasu kuma suka ce ana nufin Alfijir ne na ranar Arfa. Ala ayyi halin dai ko wanne ake nufi a cikinsu; yana nan a cikin kwana goman nan na farko. A ayoyi na gaban wannan, Allah ya yi rantsuwa da abu guda ka tsaga shi biyu (da bangare daya shi ne ranar Arfa) da kuma daya bangaren (shi ne ranar Sallah). Ikon Allah, tun daga Sahabbai har zuwa Malamai galibi haka suka fassara ayar. Akwai wasu Malaman da suka tafi a kan cewa, Allah ya yi rantsuwa ne da Shafa’i da Wutiri. Shafa’i shi ne ranar Arfa, Wutiri kuma shi ne ranar Sallar Layya. Abu guda biyu shi ake ce ma Shafa’i, abu guda daya kuma a ce masa Wutiri. Toh duk dai daya ce ta zama biyu da aka maimaita ta, haka nan aka maimaita ta ta zama uku har zuwa dubu ko sama da hakan. Ranakun Arfa da Sallah da Allah ya yi rantsuwa da su duk dai suna cikin wadannan kwana goman farko na watan Zuhajji.

Sannan wannan kwana goma na farkon watan Zuhajji tana daga cikin ranakun da Allah ya alkawarta wa Annabi Musa (AS) ya yi ibada a cikinsu domin Allah zai yi magana da shi ya ba shi sako. Wannan yana daga abin da yake kara nuna mana girman Manzon Allah (SAW) domin da Allah zai yi magana da shi ba a ce masa sai ya yi wata ibada ba tukuna. Lallai Manzon Allah (SAW) shekara uku kafin sako ya fara sauka, yakan fita zuwa Jabalun Nur, tsawon mil shida daga Makka. Idan ya zo jikin dutsen ba zai tsaya a jikinsa ba zai hau sama (ka san dai an bar ‘yan adam duka a nan), kuma idan ya hau ba zai tsaya a sama inda ake ganinsa ba a fili; zai shiga cikin kogo ne. Alhamdu lillah mun ziyarci wurin a 2007, amma har lokacin da muka je ga Birai nan suna ta tsalle-tsalle. Duk da irin ci gaban zamani a Makka amma har zuwa wannan lokacin ga Birai nan suna tsalle-tsalle a wajen, to ina ga in aka koma shekara sama da dubu da dari hudu, me za a gani a wurin? Amma nan Manzon Allah ya rika zuwa yana ibada, kuma Malamai solar yi ittifaki ba sallah yake yi ba a nan don lokacin ba ta sauka ba (duk da akwai nafilarta a Addinin Annabi Ibrahim AS), Tafakkuri yake yi, Allah shi ya san irin Zikirin da yake yi. Kuma wannan ibada da Annabi ya yi, ba a ruwaito cewa Allah ne ya wajabta masa sai ya yi kafin ya ba shi wani abu ba, kamar dai yadda al’ummarsa suke yin nafiloli na neman karin tafiya wurin Allah da izini. Amma shi Annabi Musa sai da Allah ya ce masa ya yi azumin kwana arba’in dare da rana (kamar yadda malamai suka ce).

Da farko ya yi na kwana talatin sai ya yi aswaki da iccen gabaruwa (irin na Makka) bakinsa ya yi kamshi, da ya tafi wurin ganawa da Allah; sai aka sake kara masa kwana goma saboda aswakin da ya yi, aka ce wannan warin bakin ake so ya taho da shi (amma wannan warin bakin ba a shari’ar Manzon Allah ba ne, Sahabbai solar ruwaito Manzon Allah yana aswaki da azumi”. To, Annabi Musa (AS) ya azumci watan Zulkida kwana talatin sai kuma aka kara masa da goman farko na watan Zulhajji. Wadannan kwana goma na farkon watan Zulhajji su ne Allah ya kara wa Annabi Musa (AS) ya yi azuminsu lokacin da zai gana da shi.

- Advertisement -