Fadar Shugaban Kasa: Ku Nishadantu da Bidiyon Shugaba Buhari Na Rera Wakar Bob Maley (bidiyo)

- Advertisement -

Wata mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, a ranar Litinin, 10 ga Mayu, ta shawarci ’yan kasar cewa duk da cewa kasar na cikin mawuyacin hali, amma tuni Shugaba Buhari ya fara gyara dimbin matsalolin ta hanyar ayyukan gina kasa.

jaridar legit na ruwaito.Onochie, wacce ta tuno da cewa marigayi Chinua Achebe ya rubuta wani littafi a baya mai taken ‘There was a Nation’, ta lura cewa babu wani abu sabo da zai zo da sauki. Ta watsa wani faifan bidiyo mai dauke da hoton shugaban inda yake rera wata waka wacce shahararren mawakin nan na Reggae,

@laurestar ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa:

“There was a Nation” littafi ne da shahararren mawakin nan Chinua Achebe ya rubuta wanda ya mutu a 2013.

“Tare kuma da zuwan Mai Gyara, @ MBuhari, wanda ya fara gagarumin aiki na gina kasa daga tushe.”

“Babu wani abu sabo da kalubale mai sauki ke kawo wa. “Ku nishandantu da wannar wakar almara ta Bob Marley.

- Advertisement -