Fadar Sarkin Kano Ta Fitar Da Sanarwa Gobe Litinin Za’a yi Jana’izar Mai Babban Ɗaki

0
157

Fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ta ce, za a yi jana’izar marigayiya Mai Babban Ɗaki a gobe Litinin 26 ga watan Afrilun da muke ciki.

Wannan na cikin wata sanarwa da Madakin Kano Alhaji Yusuf Ibrahim Chigari ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, ana tsammanin isowar mamaciyar filin jirgin saman Malam Aminu Kano a yau Lahadi bayan sallar magariba.

Sanarwar ta kuma ce, za a kai mamaciyar hubbaren Gidan Sarkin Kano.

Muna addu’ar Allah ya gafarta mata, ya yi mata rahama tare da magabatan mu, da dukkan musulmai.

What's On Your Mind?