Fadar Aso Villa za ta ci N10bn wajen gyare-gyare da aikin wuta a shekarar badi

0
53
  • Duk da kukan rashin kudi, za a batar da Biliyan 10 a gyaran fadar Shugaban kasa

  • Najeriya za ta kashe N4.8m wajen kayan wutar lantarki a shekara mai zuwa

  • Gwamnatin tarayya ta ware wasu miliyoyin kudi domin sayen man janareto

  • Akwai shirin kashe kusan miliyan 60 wajen hawa shafukan yanar gizo a 2021

Fadar shugaban kasar Najeriya watau Aso Villa za ta kashe Naira biliyan 4.85 domin gyaran kayan wuta a 2021, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Rahotanni solar tabbatar da cewa an ware Naira biliyan 5.3 da nufin yin wasu ‘yan gyare-gyare da kwaskwarima a ofisoshi da gidajen da ke cikin Aso Villa.

Fadar Aso Villa za ta ci N10bn wajen gyare-gyare da aikin wuta a shekarar badi

Wannan duk ya na cikin abin da aka shirya a kundin kasafin kudin shekarar 2021 wanda shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa majalisa a makon jiya.

Wadannan kudi su na kan layin ERGP 7102245 annual routine upkeep of mechanical/electrical installations of the Villa a kundin kasafin badi.

Bayan N4, 854, 381, 299 da za a batar wajen aikin wuta, fadar shugaban kasar za ta ci N153, 693, 262 a gyaren dakuna da N5, 244, 027, 241 a kan ofisoshi.

Naira miliyan 5.2 za su tafi wajen gyaran injin janareto a shekara mai zuwa. Bayan haka gwamnatin tarayya za ta batar da Naira miliyan 45 wajen mai.

Zahra Buhari – Na ji kuma na karanta game da SARS masu ban tsoro, babu hujja ga irin wannan zaluncin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ware Naira miliyan 274 domin biyan kudin shan wutar lantarki da Naira miliyan 67.1 na hawo shafukan yanar gizo.

Gwamnatin tarayya ta yi wannan lissafi ne a lokacin da ta ke kukan rashin kudi, har ma ana tunanin tattalin arzikin Najeriya zai iya dakushewa a shekara mai zuwa.

A shekarar 2021, Gwamnatin Najeriya ta ci babban buri na kashe makudan kudin da ba ta taba batarwa ba. Muhammadu Buhari ya yi kasafin N13.08tr a 2021.

A kasafin kudin na badi, shugaba Buhari ya bayyana dalilin karin kudin fetur da lantarki. Gwamnati ta na kukan cewa ta na fama da karancin kudi.

Ku na da labari cewa bashin da ake shirin karbowa a 2021, ya zarce 3% na karfin GDP.

 

 

What's On Your Mind?