Etsu Nupe Ya Bukaci Al’ummarsa Su Rungumi Koyarwar Addinin Musulunci

- Advertisement -

Etsu Nupe Ya Bukaci Al’ummarsa Su Rungumi Koyarwar Addinin Musulunci

Daga Bello Hamza,

Etsu Nupe Yahaya Abubakar ya bukaci musulmi su kasance masu da’a tare da rungumar koyarwar al’kurani mai tsarki da kuma koyarwar manzon tsira.

Etsu Nupe, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin majalisar sarakunan gargajiya na jihar Neja ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a fadarsa da ke garin Bida ranar Talata.

Basararken ya kuma nemi Musulmi su cigaba da kyakwawan ayyukan da suka koya a cikin watan Ramadan a cikin harkokin rayuwarsu.

“Dole mu cigaba da jin tsoron Allah kamar yadda muka yi a watan Ramadan.

“Ya kamata Musulmai su cigaba da ayyukan alhairi su kuma nisanci ayyukan zunubi kamar yadda suka yi a lokacin azumi.

“A cigaba da gabatar da ayyukan alhairi kamar, kyautata soyayya ga juna da kuma ciyar da marasa karfi.”

Ya ce, yakamata musulmi su guji shan giya da zina da sata da kuma dukkan ayyukan da aka haramta a tsakanin al’umma.

Ya kuma yi kira da shugabani a dukkan matakai su yi jagoranci da tsraon Allah su kuma tuna ranar da za a tayar d a u a gaban Allah don su bayyana yadda suka gudanar da mulkin su.

- Advertisement -