EFCC  Ta Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Damfara A Legas Da Abuja

0
64

EFCC  Ta Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Damfara A Legas Da Abuja

Jami’an ofishin shiyya na Hukumar EFCC da ke Abuja, solar kama mutum biyar da ake zargi da damfara ta intanet.

Wadanda ake zargin su ne, Emeto Jude Ikenna da Miracle Temple da Bictor Onyekachi da Silber Matthew Kingsley da kuma Promise Emmanuel.

Hukumar ta ce, ta cafke mutanen ne a ranar Talatar da ta wuce, a manoyarsu da ki C9, Ibanu Suite, Mabushi da F01 Kubwa, Abuja.

Kayayyakin da aka samu daga hannunsu, solar kunshi mota kirar Toyota Camry guda daya da kwamfuta daya da wayoyi.

Baya ga wannan, Hukumar ta cafke wasu mutm 18 da ake zargi da zamba ta hanyar intanet a cikin jihar Legas.

Wadanda ake zargin an cafke su ne a lokacin da suke gudanar da sintiri a rukunin gidaje na Second Gate Property, wadanda suka shiga hannun su ne, Oke-Iranla, Ajah, Lekki, da kuma Bictoria Backyard Metropolis, BGC, Lagos wadanda ake zargin su ne Ayomide Christian Balogun, Harrison Etshede, Rahim Ibrahim Ajiboye, Nwafor Ebuka, Christian Onyenachi, Egbe Emmanuel Olemuno, Okoye Charles, Moses Isaac Benjamin da kuma Abubakar Mukthar.

What's On Your Mind?