Duk jihar da na je sai mutane akalla 200 sun bani takardu in samar musu aiki – Minista Pantami ya koka

0
52

Duk jihar da na je sai mutane akalla 200 sun bani takardu in samar musu aiki - Minista Pantami ya koka

Ministan Sadarwa da tattalin arzikin Zamabi, Dr. Isa Ali Pantami ya koka da cewa ya kamata matasa su rage dogaro da takardun karatu su fita su nemi sana’a.

Ya bayyana hakane ne yayin da ke kokawa kan yawan dogaro da takardun karatu da ake yi a Najeriya.

Bidiyo: Hatsarin Dake Tattare da Dake Qafar wando Ranar Alƙiyama

Hutudole ce na ruwaito,yace akwai damarmakin samun aiki da dama wanda idan mutum ya samu kwarewa a wata sana’a zai samu, yace yawanci kasashen da suka ci gaba abin da suke yi kenan shiyasa zaka ga basu cika damuwa da aikin gwamnati ba saidai dan sadaukarwa.

Ministan ya bayyana cewa, idan ya je wata jiha kaddamar da aiki, akalla ana kai masa takardun mutane 200 ya samar musu aiki.

Ya bayyana hakane a Gombe wajan kaddamar da wata cibiyar kimiyya da fasaha da hukumar NITDA ta gina a jiya, Juma’a. Pantami ya bayyana cewa, yana kokarin ganin hada kai da abokan aikinsa dan karfafa koyon sana’a maimakon baiwa takar dar kammala karatu fifiko.

What's On Your Mind?