Duk In Da Mutum Yake A Nijeriya Halinsa Ne Ke Tafiyar Da Shi – Sarkin Yarabawan Arewacin Borno

- Advertisement -

Duk In Da Mutum Yake A Nijeriya Halinsa Ne Ke Tafiyar Da Shi – Sarkin Yarabawan Arewacin Borno

Daga Idris Aliyu Daudawa

Al’amarin kasancewa a ko wanne sako da lungu na Nijeriya a matsayin wurin zama ba tare da wata tsangwama ba, ko kuma nuna kyama kamar yadda al’amuran suke a wasu wurare, yana da alaka da kyawon haliu. Idan da ana yin haka ko kuma bin doka kamar yadda tsarin mulki ya tanada, da yanzu ‘yan Nijeriya ba su samu kan su  cikin halin da suke ciki yanzu ba. A hirar da yayi da wakilin MOBILIZED9JA A Yau Idris Aliyu Daudawa, Sarkin Yarabawan Arewacin Borno Abdullahi Abdul’aziz ya yi bayanai wadanda suka bambanta, ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

Ka iya fada wa masu karatu sunanka?
Assalamu alikum warahamtullah sunana Abdullahi Abdullasisi Sarkin Yarabawa na karamar Hukumar Abadan ta Arewacin Jihar Borno.

Zuwa yanzu shekaru nawa kake da su akan Sarautar?

Gaskiya an haife ni a Borno domin mahaifina Alhaji Abdu shi ne Sarkin Yrabawa na farko, tun zamanin marigayi chief Obafemi Awlowo lokaciun ya fito takarar shugaban kasa, ya fara kawo ziyara garin Malamfateri. Lokacin daya zo sai jirginsa ya tsaya a sama ya ce shi ba zai sauka ba, wannan gari bai yadda da shi ba, to daga nan ne aka samu yayi dan kasa- kasa. Aka ce ma shi da akwai Bayarabe dan’uwansa, wannan shi ne ya sa ya sauka, ya ce da Bayerabe aka ce ma shi da akwai Bayerabe, sai ya ce shikenan shi yazo gida. Sai ya sauka ya gudanar da yakin neman zaben sa wato kamfen, wannan kuma, a shekarar 1979 ke nan. Bayan daya kammala gudanar da kamfen nasa kuma sai ya ce ai wannan shi ne shugaban Yarabawa, sai ya kara damka shi a hannun mai martaba Shehun Barno da kuma Sarkin Malamfateri. Allah cikin ikonsa ya taimaka masa nay a yi rayuwarsa ya rasu. Wani al’amarina  shi mahaifi na shi ne bayan da aka nada shi sarauta duk inda Bayerabe ya ke, kodai kasuwanci ko wani aikin gwamnati, sai yazo gidan mu, idan kuma ya zo gidanmu, idan kuma yazo gidanmu zai karbe shiu hannu bi- biyu zai ji me ke tafe da shi aikin gwamnati ne ya kawo shi, daganan zai bashi kulawa wajen bashi masauki har zuwa lokacin da zai zama dan gari sosai. Idan kuma kasuwanci ya zo bashi da jari zai ya dauki jari ya ba shi. Bayan ya dauki jari ya bashi zai cigaba da, yin harkokin sa, to ana cikin irin hakan ne ya ci gaba da taimakawa har ma ta ksance duk wata matsala idan dai har kazo wurin shi zai share maka hawaye. Duk wanda ya zo wurin shi na shi ne bai nuan bambancin addini ko kuma kabilanci, ta haka ya ci gaba da aiwatar da ayyukan shi domin shi malamin asibiti ne wato Likita. Komai dare idan ka kwankwasa ma shi kofa  zai bude, idan aka ce shi kake nema, idan kuma kace ma shi, ya  zai fita cikin dare sai ya ce ai babu mai yi sai Allah.

Shekarun mahaifinka nawa a matsayin Sarkin Yarabawa?
Ai ya shekara fiye da talatin saboda ni da kannene ai haife mu ne a can mun kuma girma a can.

Bayan rasuwar shi mahaifinka shin Shehun Borno ne ya nada ka a sarautar Sarkin Yarabawan ko kuma Sarkin Malamfateri?
Lokacin da mahaifina ya rasu shi Sarkin Malamfateri shi ne wanda ya nada ni bisa umarnin mai martaba Shehun Borno, saboda ina zuwa gun Shehun Borno in kai ma shi gaisuwa, muna zuwa da mahaifina duk lokacin da muka shigo Maiduguri. Bayan rasuwarsa sai ya kasance wasu daga cikin yaran da mahaifina ya tarbiyattan sai suka zo suna neman ita sarautar, to Allah cikin ikon sai sai shi Shehun Bornon ya ce ai akwai dan shi, da yake zuwa da shi. To a lokacin ni na kammala makarantar Sakandare a shekarar 1995, to a lokacin ne ya ce su sarautar su ta Borno ba ta sayarwa bace. Don haka shi wannan yaron da ake zuwa wurina tare da shi na bada umarnin aje a nada shi, to daga nan aka nada nit un daga shekarar 2001 zuwa yanzun shekarar 2021. Yanzu ke nan ina da skara 20 a akan mulki.
Ko kana haduwa da wasu matsaloli wajen tafiyar da ita sarautar da aka nada ka shekaru 20 da suka wuce?
I, da akwai matsaloli amma su matsalolin wani lokacin da yadda jama’a, tunda yake an haife ni a wurin na kuma girma a wurin, kusan duk al’amura na rayuwa ta mutanen wurin tare muke yi. Dole ma a samu mtsaloli saboda wani abu zai taso na jama’a kamar daurin aure ne, suna ne, wasu bukukuwa ne, ole ne za a gaiyace ka, kuam idan kaje za ace ga Sarkin Yrabawa ya zo. Ko Shugabanni na kasa, Jiha ko karamar hukuma duk abinda ya shafe su Arewacin Borno in Allah ya yarda damu ake yi.

Ko da akwai nasarorin da ka samu a matsayin ka na Sarkin Yarabawa na Rewacin Jihar Borno?
Eh gaskiya mun samu nasara domin a lokacin dana zama Sarkin Yarabawa na fara tun daga karamar hukumar Abadan ne, har nazo na zama na Arewacin Borno, duk wadansu al’amura na jama’a wasu mun yi makaranta tare da su, wsu kannenmu wasu zau matsa su kawo kukansu mu taimaka masu, wasu mun sama masu aiki a gwamnatin tarayya, wasu sama masu abubuwan yi. “ Ka san duk inda mutum yake a Nijeriya halin sa ne yake tafiyar da shi”. Babana ya zauna lafiya da mutane , har ga shi mu ‘ya’yan shi muna cin tubarakin sa.

kananan hukumomi nawa ne suka yi Arewacin Borno?
kananann hukumomi guda goma ne kuma daga cikin goman nan babu wanda ban shiga ba, na yi makaranta ta, a Munguno iunda a can ne na kammala makarantar Sakandare a 1995, daganan kuma sai NTI wato makarantar da ake horon malaman makarantu ta karatu daga gida wadda take Damasak, sai kuma akwai garin Baga wadanda Sarakunan garin  abokaina ne tare muke, duk wani abu idan ya tashi za su gaiyace ni, zan kuma je.

- Advertisement -