Dubban ‘Yan Hijira Sun Yi Zanga-zanga Tsakanin Jihohin Nasarawa Da Benue

0
77

Dubban ‘Yan Hijira Sun Yi Zanga-zanga Tsakanin Jihohin Nasarawa Da Benue

Daga Zubairu M. Lawal Lafia

Dururuwan mutanen da suke zaune sansanin yan gudun hijira na Abagana dake yankin jihar Benue solar gudanar da zanga zanga da sanyin safiyan ralar Talata.

Masu zanga zangar solar rufe babban titin Makurdi zuwa Lafia yadda suke rera wakokin nuna rashin amincewa da kisan gillar da aka yi wa wasu mutane 10 da ake zargin makiyaya ne suka kawo harin a daren ranar Litinin.

Masu zanga zangar da akasarinsu ‘yan kabilar Tibi ne kuma mazauna sansanin ‘yan Gudun Hijirar. Sun zuba gawarwakin a kan titi suna nuna damuwa kan harin ta’addanci da aka kawo masu.

Zanga zangar ta haddasa cinkoson ababen hawa na matafiya da suka fito daga yankin Yammacin Nijeriya da kuma masu zuwa Yammacin da masu zuwa gefen jihohin Taraba.

Gwamnan Jihar Benue, Mista Samuel Ortom ya samu halartar gurin da ‘yan gudun hijirar ke zanga-zangar inda ya roke su da su bude hanyar domin motocci su rika wucewa.
A jawabinsa Gwamna Samuel Ortom ya ce; Su kara hakuri gwamnati ta sanya jami’an tsaro su gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin wannan harin da aka kai.

Ya zuwa lokacin hada wannan rohoton masu zanga-zangar solar janye daga titunan kuma komai ya koma dai-dai.

What's On Your Mind?