Dr. Gawuna Ya Jinjina Wa Kungiyar Lauyoyin Da Ke Taimaka Wa Mai Karamin Karfi

0
30

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya jinjina wa mambobin kungiyar Lauyoyin masu kare mai karamin karfi bisa jijircewar da su ke nunawa wajen tabbatar da ganin talaka ya samu adalci, kamar yadda daraktan yada labaran mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa Fagge ya shaidawa MOBILIZED9JA A YAU.

Mataimkin Gwaman ya bayyana haka ne a ranar litinin lokacin da ya karbi bakuncin wakilan kungiyar masu taimakawa wajen kare hakkin mai karamin karfi a ofishins. Gawuna ya lura da cewa ba wani abu da za a iya yi wa mai karamin karfi da ya wuce samun adalci a kowa ne lokaci bukatar irin wannan taimako ya taso.

Dr. Gawuna Ya Jinjina Wa Kungiyar Lauyoyin Da Ke Taimaka Wa Mai Karamin Karfi

“Bisa aikin da wannan kungiya ke yi, babu shakka, ba muda kalamar da za mu iya bayyana farin cikinmu, amma dai ya zama wajibi mu ci gaba da ba ku karfin guiwa ta hanyar nuna cewa lallai wannan kyakkyawan aiki ne ku ke kansa,” in ji Gawuna.

Da ya ke tsokaci kan nasarorin da wannan Gwamnati ta samu musamman kan batun rage cinkoso a gidajen gyaran hali, Gawuna ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kano na yin aiki kafada kafada da sashin lura da gidajen gyaran halaye domin tabbatar da rage cinkosu akalla sau uku a kowacce shekara.

Ya kuma jadadda cewa, hanya guda ta rage cinkoson gidajen gyaran halin shi ne kokarin rage aikata laifuka wanda hakan ne yasa Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje gina cibiyar tattara bayanai irin ta zamani wadda aka zubawa kayan aiki irin na zamani domin rage aikata

Sukar Buhari: Karon Farko Hadimin Ganduje Ya Magantu Bayan Dakatar Da Shi

miyagun laifuka a Jihar Kano.

Da ya ke jinjina wa ’ya’yan wannan kungiya kan taron da suka gudanar, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya bayyana zabar Jihar Kano a matsayin wurin da za’a gudanar da wannan da cewa kyakkyyawar dangantaka ce da ke wanzuwa tsakanin kungiyar da Gwamnatin Jihar Kano.

Daga nan sai ya tabbatarwa da mambobin kungiya ci gaba da samun goyon bayan Gwamnati domin amfanar da al’ummar Jihar Kano, kasancewar shari’a itace bangon karshe da talaka ya dogara da shi.”

Da ya ke gabatar da jawabinsa, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar, wanda kuma shi ne ya jagoranci tawaga, Barista Surajo Sa’idu cewa ya yi sunzo ofishin mataimakin Gwamnan ne domin ziyarar girmamawa tare da sa shi cikin tsare tsaren taron nasu da za’a gudanar a Jihar Kano.

“Ba abin mamaki bane lokacin da muka zabi Jihar Kano ta kasnace wurin da za a gudanar da wannan taro, sai don kasancewar Gwamnatin Jihar Kano ta bada gagarumar gudunmawa musamman a bangaren harkar ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa,” inji shi.

Tunda farko Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Barista Musa Abdullahi Lawan ya bayyana cewa shirya wannan taro da wannan kungiya tayi, an tsara shi domin fadada tunanin mambobin kungiyar musamman hanyoyin inganta ayyukansu.

What's On Your Mind?