Don Tabbatar Da Adalci A Tsakani Akwai Bukatar A Mikawa Kudu Mulki A 2023 ~ Zulum

0
57

Don Tabbatar Da Adalci A Tsakani Akwai Bukatar A Mikawa Kudu Mulki A 2023 ~ Zulum

Gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Zulum, ya fada a ranar Juma’a cewa don tabbatar da adalci, mulki ya kamata ya koma kudu a shekarar 2023.

Zulum Ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a Legas a wajen taron laccar shekara karo na 17 na Cif Gani Fawehinmi.

Tunawa da rayuwar Abubakar Tafawa Balewa da Ahmadu Bello a cikin hotuna

Zulum, wanda ya samu rakiyar wasu kwamishinoni da masu ba shi shawara na musamman, ya bayyana cewa kamata ya yi iko ya koma wasu sassan kasar. Shugaban mai ci a yanzu, shugaba Muhammadu Buhari ya fito ne daga jihar Katsina ta Arewa maso Yamma kuma yana wa’adin mulkinsa na biyu kuma na karshe.

Gwamnan ya ce, “Na gamsu cewa ya kamata a ba sauran sassan kasar damar yin shugabanci a 2023. Kamar yadda shafin Twitter na jaridar The Punch ya ruwaito.yayinda Majiyarmu na samu wannan labari daga shafin sada zumunta na dokin karfe

What's On Your Mind?