Dole Ne Mu Koyi Doke Manyan Kungiyoyi — Arteta

0
79

Dole Ne Mu Koyi Doke Manyan Kungiyoyi — Arteta

Ranar Juma’a ne Arsenal ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Eberton a wasan mako na 33 a gasar Premier League da suka fafata a filin wasa na Fly Emirates dake babban birnin kasar, London.

Sai dai kyaftin din kungiyar Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang da kuma Aledandre Lacazette ba su yi wasan ba amma kamar yadda kungiyar ta sanar ta kara da cewar watakila Martin Odegaard ya yi fafatawar kungiyar ta gaba.

Har yanzu Aubameyang bai warke daga maleriya da ya kamu a lokacin da ya je buga wa tawagar kasar Gabon wasa ba, amma ana sa ran zai koma filin atisaye a karshen wannan makon.

Shi kuwa dan wasan tawagar Faransa, Lacazette wanda ya yi rauni a wasan da Arsenal ta tashi 1-1 da kungiyar kwallon kafa ta Fulham ranar Lahadi, na yin jinya har yanzu kuma ba’a bayyana ranar da zai dawo ba.

Arsenal ta kara da cewar mai tsaron baya, Dabid Luiz na murmurewa, tana fatan zai koma atisaye mai dan sauki a mako mai zuwa sannan bugu da kari tana sa ran nan da mako biyu zuwa uku dan wasan baya, Kieran Tierney zai koma karbar horo, bayan jinyar rauni a gwiwar kafarsa sannan tuni kuma dai dan kwallon tawagar Norway, Odegaard ya ke atisaye mai dan sauki, bayan jinya da ya yi.

Arsenal tana ta tara a kan teburin Premier League da tazarar maki uku tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Eberton, wadda take ta takwas da kwantan wasa sai dai har yanzu Arsenal din wadda mai koyarwa Mikel Arteta ke jagoranta tana ci gaba da buga gasar Europa inda a halin yanzu zata buga wasan kusa dana karshe a gasar da kungiyar Villarreal.

What's On Your Mind?